Gwamnati Ta Ba da Kwana 3 a Haddace Sabon Taken Najeriya, An Fadi Fa'idar Hakan
- Yayin da aka sauya taken Najeriya, hukumar NOA ta bukaci haddace sabon taken cikin kwanaki uku domin dabbaka shi a kasar
- Hukumar ta bukaci jami'anta da ke duka kananan hukumomi 774 a Najeriya su tabbatar da haddace shi cikin awanni 72
- Wannan na zuwa ne bayan Bola Tinubu ya rattaba hannu kan sauya taken Najeriya zuwa "Nigeria We Hail Thee"
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar wayar da kan jama'a a Najeriya (NOA) ta bukaci a haddace sabon taken Najeriya cikin kwanaki uku.
NOA ta ba da wannan sanarwa musamman ga jami'anta da ke duka ƙananan hukumomi 774 a fadin Najeriya.
Bukatar NOA kan sabon taken Najeriya
Ta bukace su da su iya sabon taken Najeriya da kuma haddace shi zuwa ranar 3 ga watan Yunin wannan shekara, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta ce jami'anta da ke cikin al'umma sune kashin bayan tabbatar da sabon taken Najeriya ya zauna a ƙasar, Peoples Gazette ta tattaro.
Ta ce tana hada kai da kungiyar malaman makaranta ta NUT domin tabbatar da ƙaƙaba taken Najeriya ga dalibai a makarantu baki daya.
Daraktan yada labarai na hukumar, Paul Odenyi ya ce hukumar ta himmatu wurin dabbaka sabon taken Najeriya a kasar.
"Muna farin ciki da shiga wani sabon babi na tarihi a Najeriya"
"Tabbas wannan sabon taken Najeriya zai kara karsashi da kishin kasa a zukatan ƴan Najeriya."
- Paul Odenyi
Hukumar ta ce za ta yi dukkan mai yiwuwa domin ganin ƴan Najeriya da dama sun iya taken kasar da kuma daukar hakan da muhimmanci tare da kawo ci gaba.
Abubuwa game da sabon taken Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da dokar sauya taken Najeriya ga ƴan kasar.
An sauya taken ne daga "Arise O Compatriot" inda aka dawo da tsohon taken Najeriya da aka sani da "Nigeria We Hail Thee".
Wannan rahoto ya kawo muku muhimman abubuwa shida da ya kamata ku sani game da sabon taken Najeriya da aka dawo da shi a yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng