Kotu Ta Dakatar da Gwamna Daga Binciken Gwamnatin 2015 Zuwa 2023 da Ta Shude
- Babbar kotun jiha da ke birnin Makurdi a jihar Benue ta dakile shirin binciken tsohon gwamna, Samuel Ortom
- Kotun ta bukaci Gwamna Alia Hyacinth ya dakatar da binciken har sai kotu ta dauki mataki kan korafin da tsohon gwamnan ya shigar
- Wannan na zuwa ne bayan kafa kwamitin bincike da Alia ya yi domin bincike daga shekarar 2015 zuwa 2023
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Babbar kotun jiha a Makurdi ta dakatar da Gwamna Alia Hyacinth binciken tsohon gwmanan jihar, Samuel Ortom.
Kotun ta dauki wannan matakin ne a jiya Laraba 29 ga watan Mayu inda ta ce kwamitin da aka kafa ya dakatar da binciken.
Benue: Matakin kotu kan binciken Ortom
Har ila yau, kotun ta ce dakatarwar ta zama dole saboda jiran hukuncin da za a yi bayan shigar da korafi da Samuel Ortom ya yi kan bincikensa, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan Fabrairu ne Gwamna Alia ya kafa kwamitoci guda biyu domin kaddamar da bincike daga shekarar 2015 zuwa 2023 lokacin mulkin Ortom.
Kwamitocin da gwamnan ya kafa za su yi duba ne ga kudin da aka samu da wanda aka kashe tsawon wa'adin mulkin Ortom, cewar Daily Post.
Mai Shari'a, T. T Asua shi ya dakatar da binciken bayan lauyan Ortom, Oba Maduabuchi ya shigar da korafi kan lamarin.
Lauyan tsohon gwamna ya shigar da korafi
Maduabuchi ya ce Babban mai binciken kudin gwamnatin jihar ya riga ya yi bincike da tabbatar da asusun gwamnatin babu matsala.
Ya ce bayan kammala bincike, jami'in ya mika rahoton bincikensa ga Majalisar jihar kamar yadda tsarin doka ya tanadar.
Har ila yau, lauyan ya ce duba da tarin hujjoji da ya zayyano bai kamata a ci gaba da tuhumar Ortom ba.
Gwamna Alia ya gargadi tsofaffin gwamnoni a
Kun ji cewa Gwamna Alia Hyacinth ya gargadi tsofaffin gwamnoni jihar da su bar shi ya ci gaba da ayyukan alheri da ya fara.
Alia ya ce idan har wani tsohon gwamnan ba zai kawo shawara da za ta kawo ci gaba a jihar ba, ya ja bakinsa ya yi shiru.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng