Sojoji Sun Yi Awon Gaba da Fitaccen Malamin Addinin Musulunci da Matarsa a Abuja

Sojoji Sun Yi Awon Gaba da Fitaccen Malamin Addinin Musulunci da Matarsa a Abuja

  • Sojoji sun kutsa cikin unguwar Dei-Dei da ke Abuja inda suka yi awon gaba da malamin addinin Musulunci da matarsa
  • Malamin mai suna Muhammad Alkandawi da matarsa, Ubaidah Abdulmalik an cafke su a ranar Talata 28 ga watan Mayu
  • Sai dai ba a tabbatar da dalilin kama malamin ba inda ya ke korafin bai san mene ya aikata da aka kama shi ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar sojoji ta cafke malamin addinin Musulunci, Muhammad Alkandawi da matarsa, Ubaida Abdulmalik.

Dakarun sun kama malamin ne da iyalinsa a Dei-Dei da ke Abuja a ranar Talata 28 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Lauya ya feɗe gaskiya, ya nemowa Aminu Ado da Sanusi II mafita

Dakarun sojoji sun kama malamin Musulunci a Abuja
An shiga ɗimuwa bayan sojoji sun kama malamin Musulunci, Muhammad Alkandawi a Abuja. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

An kama na kusa da malamin Musulunci

Tun farko an kama na hannun daman malamin mutum uku a ranar Asabar 25 ga watan Mayu kafin cafke Alkandawi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta bayyana cewa malamin ya sanar a cikin wani faifan bidiyo cewa an sako sauran mutane uku da aka kama.

Malamin ya ce tun farko ya yi kokarin zuwa wurin sojojin domin sanin halin da ake ciki amma sun hana shi samun daman haka.

"Ni ba soja ba ne ko kuma wanda ya aikata ta'addanci ko garkuwa da mutane da sojoji za su kama ni kan abin da ban san da shi ba."

- Muhammad Alkandawi

Ana zargin rikicin fili ne sanadi

Rahotanni sun tabbatar da cewa malamin yana rikici da wani mai gidan dambe a yankin, Ali Zuma kan fili wanda aka kulle na tsawon mako.

Kara karanta wannan

Shahararren malamin Kano ya yi magana bayan an tashi da sarakuna 2 a gari

Sai dai ba a tabbatar ko kama malamin na da alaƙa da rikicinsa da mai gidan damben ba da ke yankin.

Malamai sun tsoma baki a sarautar Kano

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar malaman Musulunci sun shiga lamarin sarautar jihar Kano inda suka bukaci sulhu a tsakani.

Malaman sun shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya yi hankali wurin ɗaukar matakai da za su sake dagula rikici a jihar.

Daga bisani sun bukaci Tinubu ya bar ƴan jihar su nemo hanyar kawo karshen matsalar da kansu domin samun zaman lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel