Hajji: Hukumomi a Saudiyya Za Su Koro Mahajjata, NAHCON Ta Gargadi Ƴan Najeriya
- Hukumar kula da alhazai ta NAHCON a Najeriya ta gargadi mahajjata a kasar kan saɓa dokokon aikin hajji a Saudiya
- Hukumar ta ce ma'aikatar hajji da Umrah a Saudiyya ta ce za ta koro duka mahajjatan da suka saba doka da tarar Riyal 10,000
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NAHCON a Najeriya, Fatima Usara ta fitar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Makkah, Sa'udiyya - Hukumomi a kasar Saudiyya sun yi barazana korar mahajjata zuwa kasashensu.
Hukumar NAHCON ta tabbatar da haka a cikin wata sanarwa ta bakin mai magana da yawunta, Fatima Usara.
Hajji: Gargadin NAHCON ga mahajjata ƴan Najeriya
NAHCON ta ce hukumomin sun ba da wannan sanarwa ce kan wadanda ba su da katin shaida mai inganci na kasancewa a kasar, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce idan aka kama mahajjaci da laifi za a koro shi gida da kuma cin tara Riyal 10,000.
Usara ta ce wanna umarni ya yi daidai da matakin da kwamitin malaman kasar Saudiyya suke amince da shi, Tribune ta tattaro.
Matakin da hukumomi a Saudiyya suka ɗauka
"Ina mai sanar da ku gargadin ma'aikatar hajji da umra a Saudiyya kan kasancewa a kasar ba tare da katin shaida amintacce ba."
"Ma'aikatar ta ƙaƙaba tarar riyal 10,000 ga duka wadanda aka samu da laifi da kuma kora daga kasar baki daya."
"Dalilin haka, ma'aikatar harkokin kasashen waje da ke Najeriya ta samu irin wannan gargadi daga ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja."
- Fatima Usara
Sanarwar ta kuma bukaci duka mahajjata da su bi doka da oda domin tabbatar da yin aikin hajji cikin lumana.
Mahajjaciya ƴar Najeriya ta rasu a Saudiyya
A wani labarin, kun ji cewa wata mahajjaciya daga jihar Kebbi ta rasu a kasar Saudiyya a ranar Asabar 25 ga watan Mayu.
Hukumar NAHCON ita ta tabbatar da haka a cikin wata sanarwa inda ta yi addu'ar Ubangiji Sarki ya gafarta mata zunubanta.
Daga bisani an samu karin rasuwar mutane biyu daya daga jihar Kebbi sai kuma daya daga jihar Lagos.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng