Karin Albashi: An Sanya Ranar Sake Hawa Teburin Tattaunawa Tsakanin NLC Da Gwamnati

Karin Albashi: An Sanya Ranar Sake Hawa Teburin Tattaunawa Tsakanin NLC Da Gwamnati

  • Kungiyar kwadago ta NLC ta amsa gayyatar kwamitin gwamnatin tarayya kan batun mafi karancin albashi domin ci gaba da tattaunawa
  • Sau biyu hadakar kungiyoyin kwadago suna ficewa daga zaman samar da mafi karancin albashin saboda rashin gamsuwa da tayin gwamnati
  • Da farko dai an dage zaman ha sai baba ta gani, amma a yammacin nan shugaban NLC Joe Ajaero, ya tabbatar da goron gayyatar tattaunawar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Gwamnatin tarayya ta kungiyoyin kwadago za su koma teburin tattaunawa domin sake duba kan batun mafi karancin albashi da yake ta yamutsa hazo.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) Joe Ajaero ne ya tabbatar da hakan bayan karbar takardar gayyata daka shugaban kwamitin gwamnati kan mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya samu sauƙi a bukatar da ƴan ƙwadago suka gabatar kan mafi ƙarancin albashi

Joe Ajaero
An sanya ranar Juma'a domin ci gaba da tattaunawa kan mafi karancin albashi Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Nigerian Tribune ta wallafa cewa gayyatar na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun ce an tashi baran-baran tsakanin kwamitin da kungiyoyin kwadago ba tare da an cimma matsaya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Muna fatan tayin albashi mai kyau’, Ajaero

Shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Kwamred Joe Ajaero ya bayyana cewa za su halarci zaman kwamitin gwamnati kan sake duba batun mafi karancin albashi.

The Nation ta wallafa cewa amma shugaban ya yi gargadin ba za su zama ‘yan amshin shat aba, dole ne a tsefe batun yadda za su amince da shi.

Kwamred Joe Ajaero ya kara da cewa suna fatan gwamnatin za ta yi musu kyakkyawan tayin da za su iya amanna da shi.

Ana ta zama domin yanke karin albashi

Ana ta samun tsaiko kan batun albashi a kasar nan saboda gwamnati ta gaza biyan bukatar NLC na ba da N494,000 a matsayin karancin albashi.

Kara karanta wannan

Karin albashi: Don Allah kuyi hakuri ku karbi ₦60,000' gwamnati ta roki yan kwadago

Ita kuma gwamnatin ta ce N60,000 kawai za ta iya biya, lamarin da NLC ta ke yiwa kallon rashin daukarsu bukatunsu da muhimmanci.

NLC ta yi fatali da tayin albashin gwamnati

A baya kun samu labarin cewa kungiyar kwadago ta NLC da takwararta watau TUC sun sake yin fatali da tayin mafi karancin albashi da gwamnati ta yi mu su.

Ma'aikatan sun kuma rage bukatar a biya akalla N497,000 zuwa N494, 000 amma gwamnati ta ce N60,000 za ta iya ba ma'aikatan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel