Akwai Dalili: Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Ki Jawabi Gaban 'Yan Majalisar Tarayya
- Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya kare shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kin bayyana gabansu domin gabatar da jawabi
- A baya an samu sanarwa da suka yi karo da juna daga mashawartan shugaban kasar, wanda Bayo Onanuga ya sanar da zai gabatar da jawabi
- Daga baya Ajuri Ngalele ya musanta hakan, inda ya ce Onanuga bai samu izinin fitar da sanarwar ba, amma shugaban ba zai ce komai ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja - Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas ya fayyace wa 'yan Najeriya dalilin rashin jawabin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ga majalisa.
An dai yi ta samun mabanbantan bayanai kan cewa shugaban zai yi jawabi a zaman hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar nan yau Laraba.
Vanguard News ta wallafa cewa a karin hasken da ya yiwa 'yan Najeriya, shugaban majalisar ya ce Bola Tinubu zai yi jawabi a ranar dimokuradiyya ne amma ba yau ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu mabanbantan bayanai
Tun da fari an shiga rashin tabbas kan ko shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi gaban majalisar yayin da kasar nan ta cika shekaru 25 tana mulkin farar hula.
Premium times ta wallafa yadda mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya ce Tinubu ba zai yi jawabi ga zaman majalisa na hadin gwiwa yau.
Daga baya mashawarcin shugaban na musamman kan yada labarai Ajuri Ngalele ya musanta cewa Tinubu zai yi jawabi.
A jawabinsa, Shugaban majisar wakilai, Rt. Hon. Tajuddeen Abbas ya ce su ne suka yi kuskure, amma ya yi musu gyara.
Abbas ya ce shugaban zai gabatar ga jawabinsa ga 'yan kasa a ranar 12 ga watan Yuni, 2024 da ake murnar mulkin farar hula.
Gwamnati ta sauya ranar dimukuradiyya
A baya mun baku labarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya ranar dimukuradiyyar kasar nan zuwa 12 ga watan Yuni.
An sauya ranar ne daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni domin kara dabbaka dimukuradiyya ganin ranar ne aka yi zaben MK Abiola da aka soke.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng