Dangote Ya Kauracewa Dizil, Duka Motocinsa Za Su Koma Amfani da Gas a 2025

Dangote Ya Kauracewa Dizil, Duka Motocinsa Za Su Koma Amfani da Gas a 2025

  • A kokarinsa na taimakawa Bola Tinubu wurin rage dogaro da man fetur, Aliko Dangote zai koma motoci masu amfani da gas
  • Dangote ya sanar da cewa zuwa shekarar 2025, dukkan motocinsa da ke kamfanin siminti za su koma amfani da gas madadin dizil da fetur
  • Attajirin ya bayyana haka ne a jiya Talata 28 ga watan Mayu yayin taron shekara-shekara na kamfanin a garin Lagos

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kamfanin simintin Aliko Dangote ya bayyana himmatuwarsa na komawa amfani da gas a harkokin sufuri a 2025.

Kamfanin Dangote ya ce hakan na daga shirye-shiryen kau da kai wurin dogaro da man fetur kamar yadda tsarin Shugaba Bola Tinubu ya kawo.

Kara karanta wannan

Jerin alkawuran da Shugaba Bola Tinubu ya gagara cikawa cikin shakara 1

Dangote zai mayar da motocinsa masu amfani da gas
Aliko Dangote ya tabbatar da himmatuwarsa wurin rage dogaro da man fetur. Hoto: Dangote Foundation.
Asali: Facebook

Dangote ya magantu kan amfani da gas

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana haka a jiya Talata 28 ga watan Mayu a Lagos yayin taron shekara, cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin ya dauki wannan matakin ne domin taimakawa kudurin Bola Tinubu na tabbatar da rage dogaro da man fetur wanda ya yi tsada yanzu, BusinessDay ta tattaro.

"Yanzu za mu fara amfani da motoci masu amfani da gas saboda tsarin da Tinubu ya kawo na rage yawan amfani da fetur."
"Zuwa karshen wannan shekara duka motocinmu za su fara amfani da gas wanda hakan ba karamin kudi za mu zuba a harkar ba."
"Amma za mu iya yin hakan saboda muna da abin da ake nema, za mu ci gaba da daɗaɗawa wadanda muke hulda dasu."

- Aliko Dangote

Tinubu ya himmatu wurin komawa layin gas

Kara karanta wannan

Mutane sama da 20 sun sutu a harin 'bam' da aka kai masallacin Kano

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya na kokarin samar da ababan hawa masu amfani da gas domin rage dogaro da man fetur.

Gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da kaddamar da bas da adaidaita sahu 2,700 masu amfani da gas domin ragewa ƴan Najeriya radadin cire tallafin man fetur.

Tinubu ya amince da sabon taken Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar sauya taken Najeriya da ake yi a yanzu.

Dokar ta tabbatar da sauya tsohon taken Najeriya daga "Arise O Compatriot" zuwa "Nigeria We Hail Thee", a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel