Rikicin Masarautu: Majalisar Kolin Musulunci Ta Ja Hankalin Malaman Addinin Kano

Rikicin Masarautu: Majalisar Kolin Musulunci Ta Ja Hankalin Malaman Addinin Kano

  • Majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta yi magana kan rikicin masarautar Kano
  • NSCIA ta buƙaci malaman addinin musulunci a jihar da su guji yin kalaman da za ƙara dagula al'amura kan rikicin masarautar da ake ta fama da shi
  • Majalisar ƙolin ta kuma buƙaci al'ummar jihar Kano da su kwantar da hankulansu sannan kada su ɗauki doka a hannunsu kan rikicin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta gargadi malaman jihar Kano da su kiyaye harsunansu kan rikicin masarautar Kano.

NSCIA ta buƙaci malaman da su guji furta kalamai marasa kan gado kan rikicin masarautar jihar waɗanda za su iya ƙara rura wutar rikicin.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun farmaki masunta a Borno, an rasa rayukan mutum 15

NSCIA ta yi magana kan rikicin masarautar Kano
NSCIA ta bukaci malaman addinin Musulunci su kiyaye harsunansu kan rikicin masarautar Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Masarautar Kano
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren majalisar ƙolin, Farfesa Salisu Shehu ya sanya wa hannu, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nuna takaici kan kalamai masu cin karo da juna da ke fitowa daga wasu ɓangarori na malamai a jihar dangane da rikicin masarautar.

Wace kira NSCIA ta yi ga malaman Kano?

Sai dai ya yi kira ga malamai da su bar hukumomin Kano na siyasa, shari’a da al’ada su warware matsalar, rahoton Premium Times ya tabbatar da haka.

"Majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya NSCIA ta lura da kalamai masu cin karo da juna da ke fitowa daga wasu ɓangarori na malaman Kano dangane da rikicin masarautar jihar."
"A wannan mawuyacin lokacin, majalisar na kira ga malaman addinin Musulunci da su yi taka tsantsan da kuma nisantar maganganun da za su ƙara dagula al'amura da kawo rarrabuwar kawuna."

Kara karanta wannan

Kungiyar sarakuna ta ba Sanusi II shawara kan rikicin masarautar Kano

“Majalisar ta yi kira ga al’ummar Kano da su koma ga Allah da zuciya ɗaya, su kwantar da hankulansu, su guji ɗaukar doka a hannunsu. Allah ya ba mu zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasarmu ta Najeriya."

- Farfesa Salisu Shehu

Sarautar Kano: An ba Sanusi II shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiyar sarakuna ta buƙaci Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da ya fice daga fadar Sarkin Kano.

Ƙungiyar ta buƙaci Sarkin Kano na 16 da ya bi umarnin da kotu ta bayar wanda ya umarce shi da ya tattara komatsansa ya fice daga fadar wacce ke a Ƙofar Kudu cikin birnin Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng