"Nigeria We Hail Thee": Muhimman Abubuwa 6 Game da Sabon Taken Najeriya

"Nigeria We Hail Thee": Muhimman Abubuwa 6 Game da Sabon Taken Najeriya

A jiya Talata 28 ga watan Mayu, Majalisar Dattawa ta amince da kudirin sauya taken Najeriya wanda ya tsallake karatu na uku.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin inda ya zama doka wanda ke ke tabbatar da sauya tsohon taken Najeriya da ake yi.

Muhimman abubuwa 6 game da sabon taken Najeriya
"Nigeria We Hail Thee": Tinubu ya rattaba hannu kan sabon taken Najeriya. Hoto: @HouseNGR.
Asali: Twitter

Sabon taken Najeriya da aka tabbatar

A yanzu ƴan Najeriya za su koma rera "Nigeria We Hail Thee" madadin tsohon da ake rerawa na "Arise O Compatriot", cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta binciko muku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani kan sabon taken Najeriya.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Hadimin tsohon shugaban kasa ya caccaki Tinubu a karon farko

1. An yi amfani da "Nigeria We Hail Thee" daga shekarar da aka samu ƴanci a 1960 har zuwa shekarar 1978.

2. Daga bisani an sauya taken Najeriya a 1978 zuwa "Arise O Compatriot" har zuwa yanzu da aka canja.

3. A ranar 1 ga watan Oktoban 1960 aka yi amfani da "Nigeria We Hail Thee" a matsayin taken Najeriya na farko bayan tsame hannun Turawa.

4. Wata ƴar ƙasar Burtaniya, Lillian Jean Williams ita ta rubuta taken Najeriya lokacin tana kasar kafin samun ƴancin kai.

5. Frances Berda kuma ta rera taken Najeriya "Nigeria We Hail Thee" tare da saka kida.

6. A watan Mayun 2024, Majalisun Tarayya suka amince da kudirin sauya taken Najeriya inda Bola Tinubu ya tabbatar da ita a matsayin doka.

Taken Najeriya: Ƴan kasar sun yi korafi

Wasu ƴan Najeriya da dama sun kushe wannan mataki na Gwamnatin Tarayya inda suka koka kan halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Tsohuwar minista ta fusata, ta ce ba za ta komawa sabon taken Najeriya ba

Wannan mataki na sauya taken Najeriya ko kuma dawo da tsohon taken kasar na zuwa ne yayin da ake fama da rashin tsaro da talauci da hauhawan farashin kaya.

Sabon taken Najeriya

"Nigeria we hail thee,

Our own dear native land

Though tribes and tongue may differ

In brotherhood we stand

Nigerians all, are proud to serve

Our sovereign Motherland.

Our flag shall be a symbol

That truth and justice reign

In peace or battle honour'd,

And this we count as gain,

To hand on to our children

A banner without stain.

O God of all creation

Grant this our one request.

Help us to build a nation

Where no man is oppressed

And so with peace and plenty

Nigeria shall be blessed."

Majalisa ta amince da kudin taken Najeriya

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Tinubu ya rattaba hannu kan muhimmin kudirin da majalisa ta zartar

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta amince da kudirin sauya taken Najeriya daga "Arise O Compatriot" da ake amfani da shi.

Kudirin ya tsallake karatu na uku a Majalisar inda ya tabbata za a fara amfani da tsohon taken Najeriya "Nigeria We Hail Thee".

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Majalisar Dokoki ta yi a ranar 23 ga watan Mayun wannan shekara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.