Hatsarin Jirgin 'Kasa ya salwantar da rayukan Mutane 6 a 'Kasar Morocco
Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, aukuwar wani hatsarin jirgin kasa ta yi matukar muni a babban birnin Rabat na kasar Morocco dake Arewacin nahiyyar Afirka inda rayukan mutane 6 suka salwanta.
Rahotanni sun bayyana cewa, ba ya ga salwantar rayukan mutane 6 akwai kuma fiye da kimanin Mutane 70 da suka samu munanan raunuka a sanadiyar aukuwar wannan hatsari na jirgin kasa da ya kauce daga kan hanyarsa ta layin dogo.
Kamar yadda wani mai daukar hoto na jaridar AFP ya ruwaito, cikin gaggawa ma'aikatan hukumar bayar da agaji na kwana-kwana sun dira farfajiyar da wannan tsautsayi ya auku, inda suka zage dantsen su wajen kilacce gawarwakin Mutanen da suka riga mu gidan gaskiya.
KARANTA KUMA: Atiku za mu zaba a 2019 - Inyamurai dake Arewacin Najeriya
Legit.ng ta fahimci cewa, wannan hatsari ya auku a tsakanin garuruwan Kenitra da kuma Sale dake Arewacin birnin Rabat. Kafofin watsa labarai sun tabbatar da cewa Direban wannan babban jirgi na daya daga cikin mutane da ajali ya yi masa halinsa sakamakon aukuwar wannan hatsari.
Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau Talata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi lale maraba da sabbin jakadun kasashen Japan, Rasha, Brazil da kuma UAE a fadarsa ta Villa dake babban birnin kasar nan na Abuja.
Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng