Wani malamin makarantar sakandare ya dirkawa Hassana da Hussaina ciki

Wani malamin makarantar sakandare ya dirkawa Hassana da Hussaina ciki

- An kama wani malami da bashi da aiki sai ya kai daliban shi cikin ofis din shi ya dinga lalata da su, ko suna so ko basa so

- Dubun shi ta cika bayan yiwa wata dalibarshi 'yar shekara 17 ciki

A jiya Laraba ne 17 ga watan Afrilu, wata yarinya 'yar shekara 17 ta bayyanawa wata kotu yadda shugaban makarantarsu ta sakandare, Samson Adeyemo, ya dinga kwanciya da ita har sai da ya yi mata ciki.

Mutumin mai shekaru 30 a duniya, wanda shine shugaban makarantar sakandaren da yarinyar ta ke, ana tuhumar shi da zargin yiwa yarinyar ciki ita da 'yar uwarta, wadanda suke SS1 a makarantar.

An bayyana cewa mutumin ya aikata lafin a cikin shekarar 2016.

A bayanin da wacce ta kawo karar ta yi, M.S Oshodi, ta bayyana cewa malamin yana kiran yaranne zuwa cikin ofishinsa, inda ya ke kwanciya da su ya biya bukatar shi, har sai da ya yi wa daya daga cikinsu ciki.

Wani malamin makarantar sakandare ya dirkawa Hassana da Hussaina ciki

Wani malamin makarantar sakandare ya dirkawa Hassana da Hussaina ciki
Source: UGC

Matar ta ce, yarinyar ta zubar da cikin ne bayan mahaifiyarta ta taimaka mata ta kaita wurin likita.

A cewar yarinyar: "Shugaban makarantar ya ajiye gado a ofis dinsa wanda ya ke amfani da shi wurin kwanciya da su.

"A lokacin da abin ya faru ina SS1. Ranar da abin ya faru, ina zaune a ajinmu, sai Adeyomo ya shigo ya ke tambaya akwai malami a ajinmu sai muka ce aa, shine sai ya ce na biyo shi ofis din shi.

"Da muka je ofis na shin sai ya fara kirana da sunaye na soyayya, inda ya cire mini kaya na, ya yi amfani da ni sannan ya ce kada na sake na fadawa kowa abinda ya faru.

"Ya cigaba da amfani dani na tsawon lokaci, har sai da yayi min ciki.

KU KARANTA: An tura tsohon shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir gidan kurkuku

"Ni ban ma san cewa ina da ciki ba har sai da wata makociyar mu ta gane sannan ta fadawa mahaifiyarmu abinda ke faruwa.

"Mahaifiyata ce ta kira malamin, inda shi kuma ya tabbatar mata da cewar yayi min cikin. Sai ya roki mahaifiyata akan yana son cikin, ita kuma taki yarda ta ce sai an zubar dashi.

"Sanadiyyar cikin ne yasa mahaifiyata ta cire ni daga makarantar, inda ta saka ni a wata, wacce a nan na rubuta jarabawar kammala sakandare na," in ji yarinyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel