Wani Shugaban Ƴan Bindiga Ya Gamu da Ajalinsa Yayin da Suka Kai Hari a Katsina

Wani Shugaban Ƴan Bindiga Ya Gamu da Ajalinsa Yayin da Suka Kai Hari a Katsina

  • Ƴan sanda sun yi nasarar fatattakar ƴan bimdiga a lokacin da suka yi yunƙurin sace matafiya a titin Ɗandume zuwa Sabuwa a Katsina
  • Yayin musayar wuta, jam'an tsaro sun hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga, Auwalu Mahaukaci wanda ya addabi ƙaramar hukumar Ɗandume
  • Kwamishinan ƴan sanda ya yabawa jami'an bisa jajircewa da bajintar da suka nuna har suka samu wannan nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa jami'anta sun yi nasarar daƙile harin garkuwa da mutane tare da ceto wanda aka yi yunkurin sacewa a Katsina.

Rundunar ta ce yayin artabu, dakarun ƴan sanda sun hallaka wani shugaban ƴan bindiga da ake kira, Auwalu Mahaukaci.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun farmaki masunta a Borno, an rasa rayukan mutum 15

Yan sandan Najeriya.
Yan sanda sun kashe babban kasurgumin ɗan bundiga a jihar Katsina Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Getty Images

Jagoran 'yan bindiga ya bar duniya

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dakarun ƴan sanda sun gano gawar ƙasurgumim ɗan bindiga, Auwalu Mahaukaci yayin bincike a wurin da suka yi musayar wuta.

Hukumar ‘yan sanda a jihar ta bayyana cewa, Mahaukaci, ya jima yana addabar karamar hukumar Dandume da da kewaye a jihar Katsina.

Ƴan sanda sun samu nasara a Katsina

Wannan ya zo ne jim kadan bayan hedikwatar ‘yan sanda ta Dandume ta samu bayanai a ranar 28 ga Mayu, 2024, cewa ƴan bindiga sun tare titin Dandume zuwa Sabuwa.

"Bayan samun bayanan ƴan bindiga na shirin sace matafiya a titin, DPO na Dandume, SP Emmanuel Zangina, ya tara jami'ai tare da haɗin guiwar sojoji, suka kai ɗauki wurin.

Kara karanta wannan

An hallaka mutum 2 yayin gwabzawar 'yan sanda da masu garkuwa da mutane a Kogi

"Da zuwan jami'an tsaron suka yi musayar wuta da ƴan bindigar waɗanda suka arce zuwa cikin daji."

- ASP Abubakar.

Kwamishinan Katsina ya yabawa 'yan sandan

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aliyu Musa, ya yabawa ‘yan sandan bisa bajinta da jajircewar da suka nuna har suka samu wannan nasara.

Ya kuma jaddada kudirin rundunar ƴan sanda na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma a jihar Katsina, rahoton Daily Post.

Dikko Radda ya nemi taimakon Tinubu

A wani rahoton kuma Gwamnatin Katsina ta yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya taimaka domin a dawo da zaman lafiya a faɗin jihar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Nasiru Ɗanmusa ya ce a yanzu ƴan bindiga sun fara kai hari da miyagun bindigu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262