Tsohon Daraktan CBN Ya Tona Asirin Emefiele a Kotu Kan Sauya Fasalin Naira

Tsohon Daraktan CBN Ya Tona Asirin Emefiele a Kotu Kan Sauya Fasalin Naira

  • Hukumar EFCC ta gabatar da shaida a gaban babbar kotun Abuja a shari'ar tsohon gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele
  • Tsohon daraktan sashin ayyuka na CBN, Ahmed Umar, ya faɗi yadda Emefiele ya aiwatar da tsarin sauya fasalin Naira ba tare da amincewa ba
  • EFCC dai na zargin tsohon gwamnan bankin kasar da kashe biliyoyin Naira wajen buga sababbin kudin da ba su wuce N684.5m ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - A jiya Talata, 28 ga watan Mayu, 2024 aka ci gaba da sauraron shari'ar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele.

A wannan zama, tsohon daraktan ayyuka a CBN, Ahmed Umar, ya faɗawa kotu dukkan abin da ya sani game da canjin takardun kuɗin N200, N500 da N1,000.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ɗauki zafi, ya ba da umarnin a kama tsohon Sarkin Kano

Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Tsohon daraktan CBN ya bayar da shaida kan yadda aka canja fasalin Naira Hoto: Mr. Godwin Emefiele
Asali: UGC

Godwin Emefiele ya canza kudi babu izini?

Ahmed ya shaidawa kotu cewa Emefiele ya yi gaban kansa ya canja takardun kuɗi a ƙarshen 2022 ba tare da amincewar kwamitin gwamnonin bankin ba, Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai har yanzu alkali yana cigaba da sauraron karar da EFCC ta shigar a gabansa.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Emefiele

Idan ba ku manta ba hukumar yaƙi da rashawa EFCC ta sake gurfanar da Emefiele a gaban mai shari'a Maryanne Anenih ta babbar kotun Abuja ranar 15 ga watan Mayu.

Sai dai a wannan karon EFCC ta maka tsohon gwamnan a kotu ne kan tuhumar canjin Naira da buga sababbin kuɗi ba bisa ƙa'ida ba.

A tuhume-tuhumen mai lamba CR/264/2024, EFCC ta yi zargin cewa Emefiele ya aiwatar da tsarin sake fasalin Naira ba tare da amincewar majalisar gudanarwa ta CBN da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

Kara karanta wannan

Daraktoci da manyan ma'aikata sama da 300 sun rasa aikinsu a babban banki CBN

Ta kuma.tuhume shi da cewa ba tare da amincewar shugaban ƙasa ba, ya kashe N18.96bn wajen buga sababbin takardun kudi na Naira miliyan N684.5m.

A zaman baje kolin hujjoji da aka fara ranar Talata, EFCC ta gabatar da tsohon daraktan ayyuka na CBN, Ahmed Umar, a matsayin shaida na farko, The Nation ta ruwaito.

Darakta ya faɗawa kotu gaskiya

Da yake bayanin yadda aka yi, Ahmed Umar ya shaida wa kotun cewa a shekarar 2022 aka umurci sashen da yake jagoranta ya tsara sabon fasalin kuɗin Najeriya.

"Mun tsara kundin muka miƙa ofishin mataimakin gwamnan CBN mai kula da sashin ayyuka, shi kuma ya miƙa wa gwamna kuma aka sa shi cikin abubuwan da kwamitin gwamnoni zai duba."

An amincewa Emefiele canza kudi?

Shaidan ya ce an gabatar da kundin sauya fasalin Naira ga kwamitin gwamnonin domin tantancewa a ranar 26 ga Oktoba, 2022, amma kwamitin bai amince da shi ba.

Kara karanta wannan

Ana zargin shi ya shirya komai, Kwankwaso ya yi magana kan tsige sarakunan Kano

Tsohon daraktan ya shaida wa kotun cewa ya fara aiki a babban banki CBN shekaru 35 da suka gabata kuma ya yi ritaya a watan Yulin 2023. A karshe kotu ta karɓi shaidarsa.

EFCC ta gurfanar da Hadi Sirika

A wani rahoton kuma hukumar yaƙi da cin hamci ta EFCC ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika a gaban kotu.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Hadi Sirika ne tare da ɗan'uwansa, Ahmad Abubakar Sirika da wani kamfani kan badaƙalar N19.4bn.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel