Rushe Masarautu: Gwamnatin Kano Ta Sanya Sabuwar Doka Kan Masu Zanga Zanga

Rushe Masarautu: Gwamnatin Kano Ta Sanya Sabuwar Doka Kan Masu Zanga Zanga

  • Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta haramta yin kowace irin zanga-zanga a kan titunan jihar
  • Gwamnatin ta kuma umarci jami'an tsaro na ƴan sanda, DSS da NSCDC da su kama, su tsare sannan su tuhumi wanda aka samu yana yin hakan
  • Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a ranar Laraba ya sanya dokar hana duk wani taron jama'a wanda aka yi niyyar gudanar da zanga-zanga a jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.

Kara karanta wannan

Rigimar masarautar Kano: Abba ya ba jami'an tsaro sabon umarni kan masu zanga zanga

Gwamnatin Kano ta haramta zanga-zanga
Gwamna Abba ya umarci a kama masu zanga-zanga a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da sanarwar ne a shafinsa na Facebook da safiyar ranar Laraba, 29 ga watan Mayun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umarnin gwamnatin Kano kan 'yan zanga-zanga

Gwamnan Kano ya bayyana cewa ya umarci ƴan sanda, daraktan DSS, jami’an NSCDC da su kama, su tsare sannan su tuhumi duk wani ko wasu da ke gudanar da zanga-zanga a kan titunan Kano.

"Muna da sahihan bayanai da ke nuna cewa wasu ƴan jam'iyyar adawa a Kano sun shirya ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ɗalibai daga sauran jihohin Arewa maso Yamma domin tayar da hargitsi."
"Ta hanyar fakewa da nuna goyon baya ga Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da aka tsige.
"Gwamnatin jiha ta haramta kowace irin zanga-zanga, sannan za a kama duk waɗanda aka samu suna yin hakan a kan titunan Kano."

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta umarci a fitar da Muhammadu Sanusi II Daga Fadar Sarki

"Ta hanyar wannan sanarwar, muna gargaɗin ƙungiyoyin ɗalibai da ka da su bari masu son tayar da rigima da ke son kawo hargitsi a Kano su yi amfani da su."

- Sanusi Bature Dawakin Tofa

Gwamnatin ta kuma buƙaci mutanen jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Batun dawo da masarautun da aka rushe

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Inuwar Masarautar Bichi ta buƙaci majalisar dokokin jihar Kano da ta soke dokar da rushe masarautun jihar guda biyar.

Ƙungiyar ta gargaɗi gwamnatin jihar cewa rushe masarautun ka iya haifar da matsalar rashin tsaro saboda dubunnan mutanen da suka rasa ayyukansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng