Nijar da Wasu Ƙasashen Afrika Sun Sha Wutan $51m, Sun Ki Biyan Najeriya Kudin Lantarki
- Hukumar kula da hasken wutar lantarki ta bayyana cewa kasashen ketare uku ne suka ki biyanta $51.26m na kudin wutar da suka sha
- A rahoton da hukumar ta fitar, ta ce kasashen Togo, Benin da Niger sun ki biyan kudin wutar da kasar nan ke basu a shekarar 2023
- Wannan korafi na hukumar na zuwa ne yayin da su 'yan Najeriya ke fama da matsalar rashin wuta, da karin farashinta a kwanakin baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC) ta ce abokan huldarsa a kasashen ketare sun hana su kuɗin wutar da suka sha.
Hukumar ta ce akalla $51.26m take bin wadanda suka sha wutar a kasashen Niger, Togo da Benin.
The Cable ta wallafa cewa wannan bashi ne da take bin kasashen a 2023, wanda kawo wannan lokaci ba a biya ko kwabo daga ciki ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wutar lantarki: NERC ta nemi daukar mataki
Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya ta bayyana bukatar hukumomi su dauki matakin ki kakkabe halayyar kin biyan kudi.
Ta ce abokan huldarta sun rabu aji-aji, inda daya daga ciki ya ki biyan bashin N7.61b a 2023, kamar yadda thisradio now ya wallafa.
NERC ta koka kan yadda abokan huldarta suka ki biyan $16.11m a farkon 2023, yayin da aji na biyu na kwastomomin ya ki biyan N827m.
A rahoton da hukumar ta fitar, a rubu'i na biyu na shekarar 2023, kasashen sun ki biyan bashin $11.97m, su kuma aji na biyu sun ci bashin N2bn.
NERC ta magantu kan tallafin wuta
A baya mun ruwaito muku cewa hukumar kula da hasken wutar lantarki ta kasa, NERC ta bayyana cewa ba su da tabbacin za a iya dawo da tallafin kudin.
Shugaban hukumar kula da wutar lantarki na kasa, Garba Musa wanda ya bayyana hakan, ya ce har yanzu ana bin gwamnatin bashin kudi masu tarin yawa na tallafi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng