Tinubu Ya Kau da Kai ga Rikicin Sarautar Kano, Zai Yi Jawabi a Majalisun Tarayya a Abuja

Tinubu Ya Kau da Kai ga Rikicin Sarautar Kano, Zai Yi Jawabi a Majalisun Tarayya a Abuja

  • Ana tsaka da rikicin sarautar jihar Kano, Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi a taron majalisun tarayya guda biyu
  • Tinubu zai yi magana ne kan nasarar dimukradiyya shekaru 25 da majalisar tarayya ba tare da katsalandan ba
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi alfarma wurin Tinubu na tsoma baki a rikicin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu zai yi jawabi a majalisun Tarayya guda biyu a gobe Laraba 29 ga watan Mayu 2024.

Tinubu zai yi wa majalisun jawabi a tare game da nasarar dimukradiyya shekaru 25 da kuma nasarar kasancewar majalisun ba tare da matsala ba.

Kara karanta wannan

Ranar yara: Tinubu ya yi alkawura kan inganta rayuwar kananan yara

Ana tsaka da rikicin sarautar Kano, Tinubu zai yi jawabi ga majalisun Tarayya
Bola Tinubu zai gana da majalisun Tarayya 2 ana tsaka da rigimar sarautar jihar Kano. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Tinubu zai kaddamar da sabon dakin karatu

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardan majalisar, Sani Tambuwal ya fitar a jiya Litinin 27 ga watan Mayu, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tambuwal ya ce yayin taron, Tinubu zai kaddamar da sabon ƙayataccen dakin karatu da aka samar a cikin majalisar, Channels TV ta tattaro.

"Ana sanar da sanatoci da mambobin majalisar dokoki cewa akwai taron murnan cika shekaru 25 na kasancewar dimukradiyya da majalisar Tarayya."
"Bola Tinubu zai yi jawabi na musamman a taron majalisun guda biyu a gobe Laraba 29 ga watan Mayu."
"Ana bukatar dukkan 'yan majalisun biyu da su samu wurin zama da misalin karfe 9:00 na safe."

- Sani Tambuwal

Mafi yawanci irin wannan jawabi ga majalisun biyu a tare ana yi ne kawai lokacin gabatar da kasafin kudi a kasar.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Zanga zanga ta barke a fadar masarautar Gaya da majalisa ta rusa

Da hannun Gwamnatin Tinubu a rikicin Kano?

Wannan taro da Tinubu zai gabatar na zuwa ne yayin da ake tsaka da rikicin sarautar jihar Kano fiye da kwanaki biyar.

Ana zargin Gwamnatin Tarayya da hannu a ruruta rikicin sarautar jihar tun bayan tube Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna guda hudu.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin hannu a dagulewar rikicin sarautar jihar da ya ki ci ya ki cinyewa.

Abba Kabir ya nemi alfarma wurin Tinubu

A wani labarin, an ji Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nemi alfarma wurin Shugaba Bola Tinubu kan rikicin sarautar jihar.

Abba ya bukaci Tinubu da ya tsoma tare da fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga jihar domin samun zaman lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel