InnalilLahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Allah Ya Yi Wa Fitacciyar Jarumar Kannywood Rasuwa
- Jarumar Kannywood, Fati Slow Motion ta riga mu gidan gaskiya ranar Litinin, 27 ga watan Mayu, 2024 da daddare a kusa da ƙasar Sudan
- Tsohuwar jaruma a masana'antar shirya fina-finan Hausa, Mansurah Isah ce ta sanar da haka a shafinta yau Talata, ta ce za a mata janaza a can
- Mansurah ta yi wa marigayyar addu'ar Allah ya mata rahama, inda ta ce za a yi zaman makoki a gidansu da ke Unguwa Uku a garin Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finan Hausa, Fati Usman wanda aka fi sani da Fati Slow Motion ta riga mu gidan gaskiya ranar Litinin da daddare.
An tattaro cewa jarumar ta rasu ne a kusa da ƙasar Sudan kuma a can za a yi mata jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, ce ta sanar da rasuwar Fati Slow Motion a shafinta na Facebook da safiyar ranar Talata, 28 ga watan Mayu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masurah Isah ta yi addu'ar Allah SWT ya jiƙan marigayya Fati kuma ya gafarta mata kura-kuranta.
Za a yi zaman makokin 'Yar Kannywood
Mansura ta kuma bayyana cewa duk ba a nan za ayi mata jana'iza, amma za a yi zaman makoki a gidansu da ke Unguwa Uku a jihar Kano.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya yiwa Fati Slow rasuwa jiya da daddare a Abasha kusa da Sudan, a can za a yi mata sallar jana'iza.
"Amma ana zaman makoki a gidan su da ke Unguwa Uku (a jihar Kano)," in ji Mansurah Isah.
Sai dai har kawo yanzu da mu ke haɗa wannan rahoton babu cikakken bayani kan musabbabin rasuwar jarumar.
Rahama MK ta faɗi dalilin fitowa a fim
A wani rahoton na daban, an ji jarumar masana'antar Kannywood, Aishatu Auwalu ta tabbatar da cewar tana ci gaba da fitowa a fina-finai ko bayan aurenta
Aisha da aka fi sani da Rahma MK ta ce ta samu cikakken goyon baya daga wajen mijinta a lokacin da ta nuna masa aniyarta na son ci gaba da sana'arta tun kafin aurensu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng