Rikicin Kano: Abin da Sarki Sanusi II Ya Faɗawa Manyan Jami'an Tsaro a Fadarsa
- Wata majiya ta bayyana kalaman da Sarki Muhammadu Sanusi II ya faɗawa manyan jami'an tsaro a ganawar da suka yi a Kano
- Sarkin ya faɗawa shugabannin tsaro cewa umarnin kotu na hana mayar da da shi kan sarauta hayaniyar soshiyal midiya ce
- Basaraken ya ce dawo da shi kan karagar sarkin Kano da aka yi ba komai bane face gyara rashin adalcin da tsohuwar gwamnati ta masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gana da shugabannin hukumomin tsaro kan taƙaddamar sarauta da ke faruwa a jihar tun makon jiya.
A halin yanzun abubuwan da aka tattauna a wurin taron wanda ya gudana a sirrince a fadar mai martaba sarki da ke Gidan Rumfa sun fara fitowa.
Kwamishinan ƴan sanda, daraktan DSS, kwamandan rundunar sojoji da kwamandan jami'an tsaron NSCDC masu kula da Kano sun halarci taron ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abinda Sarki ya faɗawa jami'an tsaro
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, wata majiya da ta halarci taron ta ce Gwamna Abba Kabir ya fita daga wurin ya bai wa shugabannin tsaro damar ganawa da Sarki Sanusi II shi kadai.
Majiyar ta ce sarkin ya faɗawa jami'an tsaron cewa ya ɗauki umarnin kotu na dakatar da naɗinsa a matsayin hayaniyar soshiyal midiya har sai ya ga takarda a gabansa.
A cewar majiyar, Sanusi II ya faɗi haka ne bayan shugabannin tsaron sun faɗa masa shirin su na bin umarnin da kotu ta bayar.
“Sarkin ya yi jawabi na sama da da sa’a guda a wajen taron, ya shaida mana cewa abin da gwamnatin jihar ta yi shi ne adalci a kan rashin adalcin da aka yi masa a baya.
“Ya shaida mana cewa bai ga umarnin kotu da muke magana a kai ba, ya bayyana hakan a matsayin umarnin kotun soshiyal midiya har sai lokacin da ya gani a hukumance."
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa an kira taron ne saboda rikicin sarauta da ke faruwa tsakanin Sarki Sanusi II da Sarki na 15 Aminu Ado Bayero.
Aminu Ado ya fito daga fadar Nassarawa
A wani rahoton kuma Alhaji Aminu Ado Bayero, sarkin Kano na 15 ya fito daga karamar fadar da ke Nassarawa da yammacin ranar Litinin, 27 ga watan Mayu.
Tun ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu aka fara taƙaddama kan sarautar Kano bayan Gwamna Abba Kabir ya sake naɗa Muhammadu Sanusi II.
Asali: Legit.ng