Dala: Naira Ta Yi Gagarumar Galaba Mafi Girma a Cikin Watanni 2, Ta Tashi a Kasuwa
- Naira ta sake gagarumar tashi a kasuwannin gwamnati wanda shi ne mafi girma cikin wata daya da ta gabata a Najeriya
- Darajar kudin Najeriya ta karu da 10.71% a yau Litinin 27 ga watan Mayu 2024 idan aka kwatanta da kwanakin baya
- A cikin kwanakin nan Naira na sake samun galaba kan dala yayin da wasu ke danganta hakan da matakan da CBN ke dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Darajar Naira sai sake tashi take yi a cikin kwanakin idan aka kwatanta da farashin dala.
A yau Litinin 28 ga watan Mayu, Naira ta sake tashi da kusan 10.71% musamman a kasuwannin gwamnati.
Dala: Yadda farashin Naira yake a kasuwa
Rahoton FMDQ ya tabbatar da cewa a yau Litinin 27 ga watan Mayu 2024, an siyar da dala kan kudi N1,339.33.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan tashin na Naira shi ne mafi girma tun a ranar 26 ga watan Mayu da aka siyar kan N1,339.23, cewar Nairametrics.
A ranar Juma'a 24 ga watan Mayu da ta gabata an siyar da dala kan N1,482 wanda hakan ke nuna an samu karin 0.19%., BusinessDay ta tattaro.
Naira: Hada-hadar dala a kasuwar canji
Yawan hada-hadar dala a kasuwanni ya ragu da kusan 64% a yau Litinin 27 ga watan Mayu idan aka kwatanta da ranar Juma'a 24 ga watan Mayu.
A yau Litinin Dala da aka samar a kasuwa bai wuce $180m ba sabanin $556m a ranar Juma'a 24 ga watan Mayu.
Wannan tashin darajar Naira na daga cikin tasirin matakan da bankin CBN ke dauka kamar yadda wasu kwararru ke hasashe.
Bankin CBN ya kawo sabuwar doka
A wani labarin, kun ji cewa Babban bankin Najeriya (CBN) ya umarci halastattun ƴan canji da ke kasuwancin hada-hadar kudi su sabunta lasisin aikinsu.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan tsare-tsaren kudi na CBN, Haruna Mustafa, ya fitar ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, 2024.
Bankin ya kuma bukaci duk wani ɗan canji ya tabbata ya cika sharuɗɗan nau'in lasisinsa daga nan zuwa watanni shida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng