Tinubu Ya Yi Magana Kan Biyan N497,000 a Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba za ta iya biyan N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata ba a Najeriya
- Bayo Onanuga, mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai ya ce kuɗin da ƴan kwadago suka nema ya zarce tunani
- Wannan na zuwa ne bayan manyan kungiyoyin ƴan kwadago NLC da TUC sun rage bukatarsu daga N615,000 zuwa N497,000
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin tarayya karƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta ce bukatar ƴan kwadago na biyan N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba za ta yiwu ba.
A cewar gwamnatin, adadin da ƙungiyoyin ma'aikatan suka buƙata a matsayin albashi mafi ƙaranci a Najeriya ya wuce ƙima, ba ma gaskiya ba ne.
Ma'aikata na neman albashi mai yawa
Fadar shugaban ƙasa ce ta bayyana haka a wata sanarwa ranar Litinin, 27 ga watan Mayu, 2024, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce babban abin da ya kamata ɓangarori uku na kwamitin da aka kafa su fi maida hankali a kai shi ne adadin da za a iya biya bayan kowa ya amince da shi.
Tinubu ba zai iya biyan N497,000 ba
Da yake martani kan lamarin, mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya ce ma'aikata sun yiwa gwamnatin tarayya da jihohi yawa.
Idan ba ku manta ba, ƙungiyoyin kwadago NLC da TUC sun buƙaci N615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi amma daga baya suka rage zuwa N497,000.
Amma gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu sun gabatar da N57,000 a matsayin mafi karancin albashi a taron kwamitin da aka yi kwanan nan.
Yayin da yake tsokaci kan wannan cigaban, Onanuga ya ce:
"Wannan abu ne mai sauƙi, ina ganin buƙatarsu ta zarce tunani, idan da za mu tambayi Ajaero da ɗan uwanmu shugaban TUC, Osifo nawa suke biyan direbobinsu ko mafi karanci da suke biyan ma'aikatansu.
"Nawa suke biyan masu shara da goge-goge? Za su iya biyan N500,000 ko N615,000? Kun ga ba gaskiya ba ne. Ma'aikata sun yi yawa a gwamnati. Babu wani aikin ne shiyasa ake riƙe da su."
"Ba a tsammanin samun aiki mai yawa daga gare su, amma duk da haka wadannan mutane ne Ajaero ke son gwamnatin tarayya ta biya N615,000."
Obaseki ya kara albashi a Edo
A wani rahoton kuma, an ji Gwamnatin jihar Edo ƙarƙashin Godwin Obaseki ta fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a duk faɗin jihar.
Gwamna Godwin Obaseki a kwanakin baya ne dai ya yi alƙawarin ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikatan jihar zuwa N70,000 ana daf da zai bar ofis.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng