Majalisa Ta Soke Dokar da Ta Ba Tsofaffin Gwamnoni Damar Karbar Fansho Har Su Mutu
- Majalisar dokokin jihar Benue ta soke dokar da ta nemi a ci gaba da daukar dawainiyar tsofaffin gwamnoni da mataimakansu
- Dokar ta ba da umarnin biyan tsofaffin gwamnoni N25m yayin da mataimakansu za su rika karbar N15m matsayin fansho duk wata
- A zaman majalisar na yau Litinin, 'yan majalisar bisa amincewa da kudurin bai daya sun soke dokar da cewa ta sabawa muradun jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Benue - A ranar Litinin ne majalisar jihar Benue ta soke dokar da za ta ba da da umarnin ci gaba da daukar dawainiyar tsofaffin gwamnoni da mataimakansu a jihar.
Majalisar jihar ta tara a watan Mayun 2023, ta zartar da kudurin dokar kara wa tsofaffin gwamnoni da mataimakansu wa'adi na ci gaba da karbar fansho.
Majalisa ta soke dokar fanshon gwamnoni
Sai dai majalisar jihar ta 10, a zamanta na yau Litinin ta soke dokar a kan cewa akwai rashin gaskiya a yadda aka zartar da dokar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan majalisar dai sun ce dokar ta sabawa muradun jama’a, kuma sun amince da matakin ne bayan da ‘yan majalisa da dama tafka muhawara a kan dokar.
Don haka kakakin majalisar, Aondona Dajoh, ya amince da kudurin bai daya na majalisar tare da zartar da kudirin da ya rusa dokar da ta ce a ba tsofaffin gwamnoni da mataimakansu fansho har tsawon rayuwarsu.
Abin da ke cikin rusasshiar dokar fansho
1. Biyan fansho na tsawon rayuwa
Biyan kudin alawus na wata-wata daidai da asalin albashin gwamna mai ci a jihar har tsawon rayuwarsa wanda kuma za a rika cira daga asusun haraji na jihar.
Jaridar The Cable ta ruwaito Mataimakin gwamna zai ci gaba da karbar fansho na wata-wata daidai da ainihin albashin mataimakin gwamna mai ci har tsawon rayuwarsa.
2. Biyan alawus da daukar ma'aikata
Biyan alawus na Naira miliyan 25 ga tsohon gwamna da Naira miliyan 15 ga mataimakinsa a duk bayan shekara hudu.
Dokar ta bayar da umarnin siyan motocin SUV guda biyu ga tsohon gwamnan da mota daya ga mataimakin gwamna da kuma hadimai bakwai, direbobi biyu, da masu dafa abinci.
Kotu ta tabbatar da zaben Gwamna Diri
A wani labarin, mun ruwaito cewa kotun sauraron kararrakin zaben Bayelsa wanda ke da zama a Abuja ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Douye Diri.
Mai shari’a Adekunle da ke jagorantar kotun mai mutane uku a ranar Litinin ya kori karar da APC ta shigar saboda rashin cancanta da rashin hujjoji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng