Zulum Ya Bayyana Burinsa a Rayuwa Kafin Allah Ya Nufa Zai Zama Gwamna

Zulum Ya Bayyana Burinsa a Rayuwa Kafin Allah Ya Nufa Zai Zama Gwamna

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa ba babban burinsa ba ne zama gwamna
  • Gwamnan ya bayyana abin da yake son cimmawa a rayuwarsa kuma ya ce zai cigaba da ƙoƙarin kai wa ga burin nasa
  • Farfesa Zulum ya bayyana haka ne a wani taron bankwana da jami'ar Maiduguri ta shirya wa shugabanta mai barin gado

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyanawa manema labarai babban burinsa a rayuwa.

Gwmana zulum
Gwamna Zulum zai koma jami'a bayan kammala gwamnati. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna cewa gwamna Zulum ya yi jawabin ne a yayin taro bankwana da jami'ar Maiduguri ta shirya wa shugabanta mai barin gado.

Kara karanta wannan

"Babu mai daƙile mani hanyar abinci", Shugaban karamar hukuma ya gargadi gwamna

An shirya taron ne domin karrama shugaban jami'ar mai barin gado, Farsesa Aliyu Shugaba a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban burin gwamna Zulum

A cikin jawabin da gwamna Zulum ya yi a lokacin taron, ya bayyana cewa babban burinsa shi ne zama shugaban jami'ar Maiduguri.

Duk da cewa ƙaddara ce ta kawo shi zama gwamnan jihar Borno, amma babban burinsa shi ne cigaba da aikin karantarwa a jami'a.

Gwamna Zulum na da burin komawa jami'a

Har ila yau gwamnan ya ce ko da bayan ya kammala gwamnatinsa, yana da burin komawa aikin jami'a domin ganin ya cimma burinsa a rayuwa.

Ya ce yana fatan komawa jami'a ne domin ba da gudunmawa a harakar ilimi da ilmantarwa ba domin neman kudi ba, rahoton Daily Post.

Zulum ya nemi taimakon malaman jami'a

A yayin taron, gwamnan Zulum ya bukaci malaman jami'ar da su ba shi gudunmawa wajen ganin ya cimma burin nasa idan ya kammala gwamanti.

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

Ya roki malaman da su kallesa a matsayin wanda ya taba aiki a jami'a kuma tsohon dalibinsu ba wai tsohon gwamna ba.

Gwamna Zulum ya kuma bayyana irin matsalolin da jami'ar ke fuskanta da bayani kan yadda za a magance su.

Gwamna Zulum ya nada mukamai

A wani rahoton, kun ji cewa Farfesa Babagana Umaru Zulum ya naɗa sababbin hadimai 168 da mambobin majalisun gudanarwa na hukumomi 15 a jihar Borno.

Gwamnan ya sanar da haka ne a wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin Borno, Alhaji Bukar Tijjani wacce ta kunshi sunayen mutanen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng