Gwamnonin Najeriya 5 da suka yi karatu a jami’ar Maiduguri

Gwamnonin Najeriya 5 da suka yi karatu a jami’ar Maiduguri

Fitacciyar cibiyar ilimin nan dake jahar Borno, watau jami’ar gwamnatin tarayya ta Maiduguri ta bi sawun takwararta ta jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria wajen samar da shuwagabanni a Najeriya a matakai daban daban.

Legit.ng ta ruwaito a yanzu haka UNIMAID, kamar yadda aka saba kiranta ta samar da gwamnoni a Najeriya guda biyar, ma’ana tsofaffin dalibai wadanda suka yi karatun digiri a jami’ar, kuma a yanzu sun zama gwamnoni.

KU KARANTA: Dangote zai samar da lita miliyan 65 na mai da iskar gas a kullum daga matatar man fetirinsa

Gwamnonin Najeriya 5 da suka yi karatu a jami’ar Maiduguri
ikpeazu
Asali: Facebook

Wadannan tsofaffin dalibai masu albarka sun hada da Okezie Ikpeazu na jahar Abia, Abubakar Sani Bello na jahar Neja, Bala Muhammad Kaura na zababben gwamnan jahar Bauchi, Farfesa Babagana Zulum zababben gwamnan jahar Borno da kuma Ahmadu Umaru Fintiri zababben gwamnan jahar Adamawa.

A shekarar 1975 ne gwamnatin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Yakubu Gowon ce ta kafa jami’ar Maiduguri, wanda a yanzu haka take kula da cibiyoyin ilimi sama da guda biyar, kuma tana da dalibai daga kowanne sassan kasar nan.

Gwamnonin Najeriya 5 da suka yi karatu a jami’ar Maiduguri
Abu Lolo da Zulum
Asali: UGC

Baya ga gwamnonin da muka ambata, daga cikin manyan mutanen da suka halarci wannan makaranta kuma suke rike da madafan iko a Najeriya, akwai babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai da babban hafsan sojan kasa, Sadique Abubakar.

Gwamnonin Najeriya 5 da suka yi karatu a jami’ar Maiduguri
Fintiri da Bala
Asali: UGC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje yana da digiri hudu a karatun boko, inda a shekrar 1973 ne ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya inda ya samu Digirin farko a bangaren koyar da kimiyya.

Ganduje ya koma yayi Digirin Masters a Jami’ar Bayero ta Kano a harkar malanta. Ganduje ya sake komawa Zariya domin samun Digir-gir na MPA. Bayan shekaru 8 ne Gwamna Abdullahi Ganduje ya samu shaidar Digir-digir na Daktan Boko watau PhD a Jami’ar Ibadan a 1993. Ganduje yayi karatu har ya kware ne a harkar sha’ani da tsarin shugabanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel