Obasanjo Ya Taso Tinubu a Gaba, Ya Bayyana Manufofinsa 2 Masu Kuskure
- Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar nan kan Shugaba Bola Tinubu
- Obasanjo ya bayyana cewa wasu manufofin gwamnati mai ci sun zama dole a aiwatar da su, amma gwamnatin ta aiwatar da su bisa kuskure
- Tsohon shugaban ƙasar ya kuma bayyana kuskuren da Tinubu ya yi kan yadda ya tunkari juyin mulkin da sojoji suka yi a jamhuriyar Nijar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana wasu manufofin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar a matsayin waɗanda akwai kura-kurai a cikinsu.
Obasanjo ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da mayar da canjin kuɗi kan farashin bai ɗaya manufofi ne da suka dace amma an aiwatar da su bisa kuskure.
Kalaman na Obasanjo na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Tinubu take shirin cika shekara ɗaya a kan mulki, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obasanjo ya caccaki manufofin Tinubu
Tsohon shugaban ƙasar ya lissafo matakai uku na gwamnatin marasa kyau waɗanda suka haɗa da cire tallafin man fetur, canjin kuɗi, da yadda ta tunkari juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.
Mai taimakawa tsohon shugaban ƙasan kan harkokin yaɗa labarai, Kehinde Akinyemi, shi ne ya bayyana kalaman Obasanjo cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
Obasanjo ya yi kalaman ne dai a wajen wani taro da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
"Wannan gwamnatin ba ta samo hanyar da ta dace ba wajen tafiyar da tattalin arziƙi da ƙarfafa gwiwar masu zuba hannun jari su samu yardar da za su fara shigowa ba."
- Olusegun Obasanjo
Jaridar Thisday ta ce Obasanjo ya caccaki manufofin gwamnatin Tinubu na cire tallafin man fetur, mayar da canjin kuɗi kan farashin bai ɗaya da yadda ta tafiyar da juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.
Tinubu zai kori ministoci
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya raba wasu daga cikin ministocin da ke majalisar ministocinsa daga muƙamansu.
Shugaban ƙasan zai sallami ministocin ne waɗanda suka kasa taɓuka abin arziƙi a ma'aikatun da aka ba su ragamar jagoranta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng