Almajirai: 'Ba a Koyon Karatu da Bara', Sarkin Musulmi Ya Koka Kan Matsalar Arewa

Almajirai: 'Ba a Koyon Karatu da Bara', Sarkin Musulmi Ya Koka Kan Matsalar Arewa

  • Mai martaba sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya yi kira na musamman kan kawo gyara a harkar almajiranci
  • Alhaji Sa'ad Abubakar III ya yi magana ne a yayin wani taron kaddamar da makarantar karatun Alkur'ani ta zamani
  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi karin haske kan yadda aka gina makarantar da yadda za a kara wasu nan gaba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da yau da kullum.

Jihar Zamfara - Mai martaba sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya yi kira na musamman kan kawo gyara a harkar karatun allo da almajiranci.

SArkin musulmi
Sarkin Musulmi ya yi kira kan gyara tsarin karatun allo. Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sarkin ya yi jawabin ne a wani taron bude makarantar Alkur'ani ta zamani a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Sarki Muhammadu Sunusi II ya jagoranci sallarJuma'a a fadar Gwamnatin Kano

An kaddamar da makarantar ne a karamar hukumar Gummi kuma an karrama mai martaba sarkin Musulmi bisa sanyawa makarantar sunansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar sarkin musulmi kan almajiranci

A yayin taron mai martaba sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ya ce lallai harkar karatun allo al'amari ne mai kyau a cikin al'umma.

Ya kara da cewa saboda muhimmancin karatun ne ma ya baro abubuwa masu muhimmanci ya taho har jihar Zamfara domin a yi bikin tare da shi.

Sarkin Musulmi ya yi kira kan bara

Duk da cewa Sarkin ya yabi karatun allo amma ya ce akwai bukatar kawo gyara a harkar barace-barace da almajirai ke yi, rahoton Daily Post.

Ya ce barin yara suna bara da sunan neman ilimi ba abu bane da zai haifar da da mai ido kuma ba zai sa yaran su samun ilimi ba.

Kara karanta wannan

Tarihi ya maimaita kansa: Yadda aka fara raba masarautu da rusa su a jihar Kano

Za a kara makarantun almajirai a Zamfara

A yayin da yake jawabi a wajen taron, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa za a kara gina makarantun almajirai na zamani a Kaura Namoda da Gusau.

Ya kara da cewa an yi hadaka ne tsakanin bankin duniya da jihar Zamfara wajen samar da makarantar da aka kaddamar din.

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya yi kira

A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Musulmi ya gargadi hukumomi kan matsifar da take tunkaro Najeriya idan har ba a dauki mataki ba.

Sultan Sa’ad Abubakar ya ce a yanzu mutanen Najeriya sun fusata lokaci kawai suke jira domin daukar mataki saboda haka ya ce dole a daga wajen neman mafita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng