Rikicin Masarauta: Bayan Ya Yi Barazana, Gwamnatin Kano Ta Ba Nuhu Ribadu Hakuri
- Gwamnatin jihar Kano ta janye zargin da ta yi wa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na hannunsa a rikicin masarauta
- Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo wanda ya yi zargin ya nemi afuwar Malam Nuhu Ribadu
- Aminu Abdulsalam ya bayyana cewa yaudarar gwamnatin aka yi kan bayanan da aka ba ta wanda hakan ya sanya ta zargi Ribadu da hannu wajen dawo da Aminu Ado Bayero zuwa Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta nemi afuwar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.
Gwamnatin jihar dai ta hannun mataimakin gwamnan jihar ta zargi Nuhu Ribadu da hannu a rikicin masarautar jihar.
Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zargi Nuhu Ribadu da taimakawa wajen dawo da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, zuwa Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano: Wace barazana Ribadu ya yi?
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron dai ya musanta hannu a lamarin inda ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan mataimakin gwamnan.
A cikin wata takarda, lauyoyin Ribadu sun bukaci neman afuwa daga mataimakin gwamnan jihar kan wadannan kalamai da ya yi na ɓatanci.
Gwamnatin Kano ta ba Nuhu Ribadu haƙuri
Sai dai Abdulsalam Gwarzo ya janye zarge-zargen nasa a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Mataimakin gwamnan ya kuma ba Nuhu Ribadu haƙuri, yana mai cewa an ba gwamnati bayanai ne marasa ƙamshin gaskiya, rahoton TVC ya tabbatar.
"Mun ƙara yin bincike kuma mun gano cewa an yaudare mu sosai, kuma a madadin gwamnatin jihar muna so mu nemi afuwar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro."
- Aminu Abdulsalam Gwarzo
Batun rikicin masarautar Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta musanta cewa tana da hannu a rikicin da ke faruwa a masarautar Kano.
Kakakin rundunar Onyema Nwachukwu a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa jami'an rundunar da aka tura zuwa fada, an kai su ne domin hana karya doka da oda ba tabbatar da umarnin kotu ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng