“Na Karbi Kaddara”: Sarkin Gaya Ya Yi Magana Bayan Gwamnatin Kano Ta Tube Rawaninsa
- Tsohon Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya amince da tsige shi daga mukaminsa a matsayin “mukaddari daga Allah”
- Jawabin na sa na zuwa ne biyo bayan soke dokar da a baya ta daukaka manyan sarakuna biyar ciki har da shi Alhaji Abdulkadir
- Tsohon sarkin ya kuma ce ba zai kalubalanci matakin a kotu ba kuma idan aka ba shi wani mukamin zai karba da hannu biyu-biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gaya, jihar Kano - Tsohon Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Abdulkadir, daya daga cikin sarakuna 5 da gwamnatin Kano ta rusa masarautun su ya ce sun karbi wannan hakan a matsayin kaddara.
A ranar Alhamis, Gwamna Abba Yusuf ya kori dukkan sarakunan da Ganduje ya nada a 2019 da suka hada da Gaya, Karaye, Rano, Bichi da kuma sarkin Kano.
Sarkin Gaya ya dauki kaddara
Da yake mayar da martani kan matakin da gwamnan ya dauka a wata hira da BBC Hausa, Sarki Abdulkadir da aka tsige ya ce ba ya jin haushin kowa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa ba shi da wani shiri na kalubalantar matakin a kotu kuma idan har aka kira shi domin yin aiki a wani matsayi zai karba da hannu biyu-biyu.
"Tabbas duk wanda irin hakan ta same shi ba zai ji dadi ba, to amma Allah ne ya kawo ka, kuma shi ne wanda ya kawo karshenka a mukamin."
- A cewar Alhaji Aliyu Abdulkadir.
Zanga-zanga ta barke a Gaya
Tun da fari, mun ruwaito cewa zanga-zanga ta barke a karamar hukumar gaya kan rusa masarautar Gaya da gwamnatin jihar Kano ta yi.
Masu zanga-zangar sun yi kira ne ga Gwamna Abba Yusuf da ya mayar da sarakunan da ya tsige tare da tsige Muhammadu Sanusi daga kan kujerar Sarkin Kano.
Sabuwar zanga-zanga ta barke a Nasarawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa sabuwar zanga-zanga ta mamaye karamar hukumar Nasara inda mutane ke nuna bacin rai kan matakin gwamnatin jihar na kin bin umarnin kotu.
Masu zanga-zangar sun nemi gwamnatin jihar Kano da ta bi umarnin babbar kotun tarayya na dakatar da aikwatar da dokar da rusa masarautun biyar na jihar.
Asali: Legit.ng