Sarkin Kano: Jami'an Tsaro Sun Dauki Mataki Kan Aminu Ado Bayero
- An jibge jami'an tsaro a hanyar da ke zuwa fadar da tsohon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero yake zaune
- Jami'an tsaron waɗanda suke da tarin yawa sun rufe hanyar da ke zuwa fadar wacce ke a Nasarawa a cikin birnin Kano
- Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikici kan sarautar Kano biyo bayan rattaɓa hannu kan sabuwar dokar masarautun Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - An jibge jami'an tsaro a hanyar da ke zuwa fadar da Alhaji Aminu Bayero yake zaune a cikin birnin Kano.
Tun bayan dawowarsa birnin Kano bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuɓe shi daga sarautar Kano, tsohon Sarkin na Kano yana zaune ne a gidan sarki da ke Nasarawa.
Jaridar TheCable ta kawo rahoto cewa jami'an tsaro sun rufe hanyar da ke zuwa fadar wacce ke a Nasarawa cikin birnin na Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wasu hotuna da shafin jaridar na X ya watsa, an ga tarin motocin jami'an tsaro girke a hanyar da ke zuwa cikin gidan sarkin da ke Nasarawa.
Ba a san dai dalilin jibge jami'an tsaron ba amma hakan dai bai rasa nasaba da rikicin sarautar da ke faruwa a jihar Kano.
Aminu Ado Bayero ya dawo Kano
Alhaji Aminu Ado Bayero dai ya dawo birnin Kano ne da safiyar ranar Asabar, kwanaki biyu bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaɓa hannu kan dokar da ta tuɓe shi daga sarauta da sauran sarakuna huɗu da aka ƙirƙiro a lokacin Ganduje.
Bayan ya dawo birnin Kano, Gwamna Abba ya umarci jami'an tsaro da su cafke shi bisa zargin cewa yana ƙoƙarin kawo rikici a jihar.
Sai dai, jami'an tsaron ba su yi hakan ba inda suka ce za su yi biyayya ga umarnin kotu wanda ya hana naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano.
Daga baya shugabannin tsaro a jihar sun kai ziyara a gidan sarkin na Nasarawa inda suka gana da tuɓaɓɓen Sarkin na Kano.
An tabbatar da jibge jami'an tsaro
Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin birnin Kano mai suna Ibrahim Zulkiful wanda ya tabbatar da girke jami'an tsaro a gidan Sarkin da ke Nasarawa.
Ya bayyana cewa jami'an tsaron sun hana wucewa ta gaban gidan Sarkin domin samar da tsaro.
Ya yi nuni da cewa jibge jami'an tsaron bai rasa nasaba da hatsaniyar da wasu suka so su tayar a gidan Sarkin na Nasarawa.
Jami'an tsaro sun gana da Sanusi II
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabannin tsaro a jihar Kaduna sun gana da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Shugabannin tsaron sun gana da Sarkin na Kano ne tare da gwamnan a fadar Sarkin ta Gidan Rumfa da ke cikin birnin Kano.
Asali: Legit.ng