Sarkin Kano: Matasan Arewa Sun Rubuta Wasika Ga Tinubu, Sun Yi Muhimmin Gargadi
- Ƙungiyar matasan Arewa ta akka da wasiƙa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan rikicin sarautar Kano
- Ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasan da ya yi taka tsan-tsan da wasu da ke cikin gwamnatinsa masu son kawo rikici a jihar Kano
- Ta yi gargaɗin cewa yunƙurin dawo da Aminu Ado Bayero kan sarauatar Kano ba komai ba ne illa ƙoƙarin yi wa tanadin doka karan tsaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Ƙungiyar majalisar matasan Arewa ta rubuta wasiƙa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan rikicin sarautar Kano.
Ƙungiyar ta shawarci Shugaba Tinubu da ya yi taka tsan-tsan da wasu da ke cikin gwamnatinsa da ke shirin haifar da rikici a jihar Kano.
Jaridar The Punch ta ce wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 25 ga watan Mayun 2024, tana ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Dakta Ali Idris da sakatarenta, Dakta Garba Abdulhafiz.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasiƙar kuma an tura kwafinta zuwa ga ofishin majalisar ɗinkin duniya, ƙungiyar tarayyar Turai, ƙungiyar ECOWAS da sauransu, rahoton jaridar Leadeship ya tabbatar.
Wane gargaɗi aka yi wa Tinubu?
Wasiƙar ta yi nuni da cewa sauyin da aka samu a dokar masarautun jihar ya samu ne sakamakon dokar da majalisar dokokin jihar ta amince da ita, sannan duk wani ƙoƙarin sauya dokar zai haifar da rikici.
Ƙungiyar ta bayyana cewa yunƙurin dawo da Aminu Ado Bayero kan sarauta ba komai ba ne face ƙoƙarin yi wa doka karan tsaye.
Wani ɓangare na wasiƙar na cewa:
"Wannan mummunan lamarin abin kunya ne ga gwamnatinka da ƙimarka a matsayin wanda a koda yaushe yake bayyana kansa a matsayin ɗan dimokuraɗiyya."
"Tsoronmu shi ne gwamnatinka da waɗanda ka ba muƙamai, za a iya yi musu kallon mutanen da ba su mutunta mulkin dimokuraɗiyya da kundin tsarin mulki."
"Muna son mu jawo hankalinka a wannan gaɓar cewa Kano ta kasance cikin zaman lafiya."
"Sannan duk wani ƙoƙarin kawo hargitsi a jihar ta hanyar biyewa wasu tsiraru masu son kansu saɓanin abin da mutane miliyan 20 suke so, zai haifar da ruɗani da rikici kuma zai ɓata sunsn gwamnatinka."
Rawar da Tinubu ya taka a naɗin Sarkin Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana rawar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya takaa wajen dawo da shi kan sarauta.
Sarkin na Kano ya bayyana cewa shugaban ƙasan bai yi katsalandan ba wajen dawo da shi kan sarauta duk kuwa da matsin lambar da aka yi masa kan ya yi hakan.
Asali: Legit.ng