Malaman Musulunci Sun Tsoma Baki a Rikicin Sarautar Kano, Sun Gargadi Tinubu

Malaman Musulunci Sun Tsoma Baki a Rikicin Sarautar Kano, Sun Gargadi Tinubu

  • Yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar a Kano kan sarautat jihar, Majalisar malaman Musulunci sun magantu kan matsalar
  • Malaman sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya bi lamarin a hankali wurin daukar matakai da zasu dakile tashin-tashina da rikici
  • Gamayyar malaman sun kuma shawarci Tinubu da ya cire hannunsa kan lamarin ya bar yan jihar Kano su sasanta tsakaninsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Majalisar malaman jihar Kano ta yi martani kan abin da ke faruwa a jihar kan matsalar sarautar da ke faruwa.

Malaman sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauki matakan da suka dace domin kawo karshen matsalar ba tare ta jawo tashin hankali ba.

Kara karanta wannan

Kano: Lamura sun dagule bayan matasa dauke da makamai sun cika fadar Sarki, bayanai sun fito

Malaman Musulunci sun gargadi Tinubu kan rikicin sarautar Kano
Majalisa Malaman Musulunci a Kano sun ba Bola Tinubu shawara kan matsalar da ke faruwa a jihar. Hoto: Aminu Ado Bayero, Asiwaju Bola Tinubu, Sunusi Lamido Sanusi.
Asali: Facebook

Kano: Shawarar malaman Musulunci ga Tinubu

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Malaman Musuluncin suka fitar a yau Asabar 25 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren sadarwa, Hassan Sani Tukur ya wallafa sanarwar a shafinsa na X.

Malaman sun nuna damuwa kan yadda lamarin ke neman jawo tashin hankali inda suka bukaci Tinubu da ya bar yan jihar su shawo kan lamarin ba tare da amfani da karfi ba.

Takardar da fitattun malaman Musulunci 18 suka sanyawa hannu sun hada da Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa da Sheikh Ibahim Khalil da sauransu.

Kano: Malaman Musulunci sun ba da shawara

Har ila yau, malaman sun bukaci dukkan bangarorin da ke cikin lamarin da su bi hanyar lalama domin dakile tashin hankali a jihar.

"Kano na daga cikin jihohi da ake zaman lafiya, idan ba a yi hankali wurin shawo kan matsalar ba yana iya rikidewa zuwa tashin hankali."

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

"Ya kamata Tinubu ya dauki matakan dakile tashin hankali a jihar, yayin da majalisa ke da hurumin yin doka, gwamnatin jihar na bukatar goyon bayan Gwamnatin Tarayya."
"Majalisa ta yi doka, gwamna ta sanya hannu ta tabbata, bai kamata a samu adawa da dokar ba, mu muna Allah wadai da duk wani shirin da zai kawo rashin zaman lafiya."
"A matsayin Tinubu na shugaba, ya kamata ya bar ƴan Kano su shawo kan matsalar da kansu, a matsayinmu na masu ruwa da tsaki, muna ba shugaban kasa tabbacin zama da dukkan bangarorin biyu."

- Majalisar malamai

Ribadu ya nesanta kansa Sarkin Sarautar Kano

A wani labarin, kun ji cewa Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya magantu kan rikicin sarautar jihar Kano.

Ribadu ya musanta hannu a cikin zargin da ake yi kansa cewa yana kokarin dawo da Aminu Ado Bayero kan karaga a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.