"Babu Wanda Ya Fi Ƙarfin Doka," Sarkin Kano da Aka Tsige Ya Mayar da Martani Mai Zafi

"Babu Wanda Ya Fi Ƙarfin Doka," Sarkin Kano da Aka Tsige Ya Mayar da Martani Mai Zafi

  • Sarki Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya mayar da martani kan rikin sarauta a karon farko tun bayan komawa gida
  • Tsigaggen sarkin ya bayyana cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka don haka ya yi kira ga al'umma su kwantar da hankulan su kuma su zauna lafiya
  • Ya bayyana cewa jihar Kano da na matukar tasiri a Najeriya, inda ya nemi mahukunta su yi adalci kan abubuwan da ke faruwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15, ya ce babu wani mahaluƙi da ya fi karfin doka, yana mai kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya bayyana rawar da Tinubu ya taka wajen dawo da shi kan sarautar Kano

Da yake jawabi a karamar fadar da yake zaune a ciki tun lokacin da ya dawo jihar bayan tsige shi, Aminu ya ce gaskiya za ta yi halinta.

Alhaji Aminu Ado Bayero.
Sarkin Kano na 15 ya buƙaci al'umma su kwaɓtar da hankalinsu Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Aminu Ado ya buƙaci a zauna lafiya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Aminu Ado Bayero na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina kira ga jama’a da su ci gaba da bin doka da oda yayin da zamu ci gaba da jiran hukuncin da kotu za ta yanke kan wannan rikici.
"Muna kira ga hukuma da ta yi adalci a wannan lamarin, Kano jiha ce mai matukar tasiri a Najeriya. Duk abin da ya shafi Kano ya shafi Najeriya baki ɗaya. Allah ya zaunar damu lafiya a Kano.
"Muna rokon Allah ya bamu shugabanni masu son gaskiya da adalci saboda adalci shi ne jagora a kowane abu. Gaskiya za ta bayyana domin ba wanda ya fi ƙarfin doka."

Kara karanta wannan

Ribadu yana kokarin dawo da Aminu Ado karfi da yaji kan karaga? an gano gaskiya

Ya kuma ƙara da cewa zai karbi duk abinda doka ta yanke, kana ya ƙara jinjina da yabawa ɗaukacin al'ummar da suka nuna damuwarsu kan halin da ake ciki.

A cewarsa, za su ci gaba da rokon Allah ya kawo zaman lafiya mai ɗorewa a jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.

An tsaurara tsaro a gidan gwamnati

A wani rahoton kuma Jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana sun mamaye muhimman wurare a gidan gwamnatin jihar Kano yau Asabar, 25 ga watan Mayu

Wannan mataki na ƙara tsaurara tsaro na zuwa ne a lokacin da taƙaddama kan kujerar Sarkin Kano ke ƙara dagulewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262