'Yan Sanda Sun Cafke Kasurgumin Dan Bindiga da Ceto Mutum 3 a Kaduna

'Yan Sanda Sun Cafke Kasurgumin Dan Bindiga da Ceto Mutum 3 a Kaduna

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta sanar da cewa jami'anta sun samu nasarar cafke wani ƙasurgumin ɗan bindiga a jihar
  • Kakakin rundunar ASP Mansir Hassan wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ya ce an cafke ɗan bindigan ne a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar
  • Jami'an tsaron sun kuma yi nasarar kuɓutar da wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su a garin Kidandan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Kaduna sun cafke wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Muhammad Bello.

Jami'an ƴan sandan sun cafke ɗan bindigan ne a wani samame da suka kai garin Kidandan da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan watanni 17, ƴan sanda sun yi galaba kan ƴan bindigar da suka sace 'yaƴan ɗan majalisa

'Yan sanda sun cafke dan bindiga a Kaduna
'Yan sanda sun cafke kasurgumin dan bindiga a Kaduna Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Ƴan sanda sun cafke ɗan bindiga a Kaduna

Ɗan bindigan mai shekaru 30, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, makusanci ne ga ƙasurgumin ɗan bindiga Dogo Haliru, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama wanda ake zargin ne bayan jami'an ƴan sandan sun samu sahihan bayanai.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Asabar.

An ceto mutane daga hannun ƴan bindiga

Rundunar ƴan sandan ta kuma kuɓutar da mutane uku da aka yi garkuwa da su a yayin wata arangama da ƴan bindiga a kan hanyar Kidandan zuwa Dogon Dawa a ƙaramar hukumar Birnin-Gwari.

A cewar sanarwar, jami’an ƴan sandan da ke Kidandan sun samu kiran waya cewa ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare hanyar Kidandan zuwa Dogon Dawa inda suka yi garkuwa da mutanen da ba a san adadinsu ba.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan daba suka hallaka ma'aikacin lafiya a wajen bikin aure a Neja

Cikin gaggawa DPO na yankin ya tura tawagar ƴan sanda da ke aiki a Operation Whirl Punch a Galadimawa, zuwa wurin inda suka fafata da ƴan bindigan.

Duk da ƴan bindigan sun lalata tayar motar ƴan sandan, jami'an tsaron sun yi nasarar ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su.

Ƴan sanda sun cafke ɓarayi

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Neja sun yi nasarar kama ɓata garin da ke musanyawa mutane katin cirar kudi na ATM.

Jami'an ƴan sandan sun kama wasu mutum biyu ɗauke da katinan ATM guda 42 da su ka sace daga hannun bayin Allah a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng