Tsautsayi: Tankar Mai ta Fadi, ta Kama da Wuta Ganga Ganga

Tsautsayi: Tankar Mai ta Fadi, ta Kama da Wuta Ganga Ganga

  • Wata tankar mai ta fadi a safiyar yau a yankin Ibafo/Aseese dake babban titin Lagos zuwa Ibadan wanda ya haddasa tsaiko wurin zirga-zirgar ababen hawa
  • Jami’in hulda da jama’a na hukumar ya tabbatar da bin dokokin hanya a jihar Ogun Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da hakan a safiyar yau, inda ya ce motar ta kama da wuta
  • Jami'in ya kara da cewa zuwa yanzu an shawo kan matsalar domin har an fara samun dawowar zirga-zirgar ababaen hawa bayan an kashe wutar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ogun- A safiyar yau ne wata mota dauke da man fetur ta fadi kuma ta kama da wuta a yankin Ibafo/Aseese dake babban titin Lagos zuwa Ibadan.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun yi magana kan sake maɗa Sanusi II a matsayin Sarkin Kano

Hukumar tabbatar da bin dokokin hanya a jihar ta tabbatar da cewa tun da misalin karfe 7:00 na safiyar yau motar ta fadi.

Prince Dr. Dapo Abiodun - MFR
Tankar Mai ta kife a tsakiyar titi Hoto: Prince Dr. Dapo Abiodun - MFR
Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa ba a samu asarar rayuka ba, amma lamarin ya kawo tsaiko a zirga-zirgar ababen hawa a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shawo kan wutar tankar mai

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ya tabbatar da bin dokokin hanya a jihar Ogun Babatunde Akinbiyi, ya ce jami’anta sun shawo kan wutar da ta tashi a titin Ibafo/Aseese.

Wutar ta tashi ne bayan wata mota mai dauke da man fetur ta fadi a tsakiyar titi, amma kakakin ya ce an shawo kan wutar da wuri.

Motar man ta fadi da misalin karfe 7.00 na safe, kuma an shawo kan matsalar da misalin karfe 8.30, kamar yadda Tribune Online ta wallafa.

Kara karanta wannan

"Wannan ba cigaba ba ne': Hadimin Buhari ya caccaki Majalisa kan rusa masarautun Kano

Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da cewa yanzu haka an fara samun dawowar zirga-zirgar ababen hawa kamar yadda yake a baya.

Ogun: Hadarin mota ya kashe mutane

A baya mun kawo muku labarin cewa hadurran mota a wurare daban-daban da ya rutsa da mutane a jihar Ogun ya jikkata mutane da dama.

Jami'ar hulda da jama'a ta hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce wasu mutane 21 sun jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel