Bidiyon Yadda Muhammadu Sanusi II Ya Ke Maraba da Kanawa a Fada Duk da Halin da Ake Ciki

Bidiyon Yadda Muhammadu Sanusi II Ya Ke Maraba da Kanawa a Fada Duk da Halin da Ake Ciki

  • Ta tabbata a yanzu an ware tsakanin masu goyon bayan Muhammadu Sanusi II da tsohon Sarki Aminu Ado Bayero a Kano
  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi fatali da halin da ake ciki inda ya fito domin tarbar dandazon jama'a a fadarsa
  • Wannan na zuwa ne yayin da jami'an tsaro suka gana da tsohon sarki Aminu Ado Bayero a fadarsa dake Nasarawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin ake ci gaba da zaman dar-dar a jihar Kano kan kujerar sarautar jihar, Sarki Muhammadu Sanusi II ya isa fadarsa.

Sarkin ya shiga fadarsa duk da kokarin da ake yi daga sama domin hana tabbatar da shi a matsayin Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi biyayya ga kotu, 'har yanzu aminu ado bayero ne sarkin Kano'

Sarki Sanusi II ya isa fadarsa inda ya yi gaisuwa ga dandazon Kanawa
Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi maraba da jama'a a fadarsa da ke Kano. Hoto: Sanusi Lamiso Sanusi.
Asali: UGC

A cikin wani faifan bidiyo da Daily Trust ta yada, an gano Sarkin yana maraba da Kanawa da suka yi dandazo domin tarbarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon Sarki Sanusi II a fadarsa

Kwamishinan yan sanda ya magantu

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar kan sahihancin kujerar Sanusi II bayan hukuncin kotu.

Kwamishinan yan sanda a jihar, Hussaini Gumel ya tabbatar da cewa za su bi umarnin kotu da ta haramta tube Aminu Ado Bayero.

Wannan ya biyo bayan sanarwar da rundunar yan sanda ta fitar cewa tana tare da matakin da kotu da dauka a kowane hali.

Kwamishinan ya sandan jihar ya kuma gargadi dukkan masu niyyar tayar da tarzoma da su shiga ruwan hankalinsu sabioda ba za su ji ta dadi ba.

Babbar kotun Tarayya ta dakatar da mayar da Muhammdu Sanusi II kan kujerarsa bayan tube Aminu Ado Bayero.

Kara karanta wannan

Kano: Lamura sun dagule bayan matasa dauke da makamai sun cika fadar Sarki, bayanai sun fito

Sojoji sun ba Aminu Ado kariya

A wani labarin, kun ji cewa Dakarun sojoji sun ba tsohon Sarki Aminu Ado Bayero kariya a Kano bayan tube shi a sarauta.

Daukar matakin ya biyo bayan umarnin Gwamna Abba Kabir na cafke tsohon sarkin da ya shigo garin Kano.

Wannan na zuwa ne yayin da jami'an tsaro suka ki bin umarnin Abba Kabri na cafke tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel