Kano: Lamura Sun Dagule Bayan Matasa Dauke da Makamai Sun Cika Fadar Sarki, Bayanai Sun Fito

Kano: Lamura Sun Dagule Bayan Matasa Dauke da Makamai Sun Cika Fadar Sarki, Bayanai Sun Fito

  • Abubuwa sun fara rincabewa yayin da aka fara zaman dar-dar a Kano bayan matasa sun cika harabar fardar Sarkin Kano da makamai
  • Mafi yawan matasan sun haɗa da masu goyon bayan tsohon Sarki, Aminu Ado Bayero da kuma Muhammad Sanusi II
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya umarci kama tsohon sarkin bayan shigowarsa garin Kano a yau Asabar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - An shiga fargaba yayin da rahotanni ke nuna cewa matasa sun cika harabar fadar Sarkin Kano.

Matasan da suka haɗa da ƴan Kwankwasiyya da kuma masu goyon bayan tsohon Sarki Aminu Ado Bayero sun ja daga a harabar fadar.

Kara karanta wannan

Kano: Sojoji sun ja daga yayin da Abba Kabir ya umarci cafke Aminu Ado Bayero

Matasa sun yi wa fadar Sarkin Kano tsinke
Ana zaman dar-dar yayin da matasa ta kowane ɓangare suka cika harabar fardar Sarkin Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Aminu Ado Bayero.
Asali: Facebook

Matasa sun cika fadar Sarkin Kano

Wannan na zuwa ne yayin da Sarki Muhammadu Sanusi II zai shiga fadar a yau Asabar 25 ga watan May, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mafi yawa daga cikin matasan suna dauke da makamai inda suke wake-wake na goyon baya ga tsohon Sarki yayin da wasu ke sanye da jar hula na goyon bayan Muhammadu Sanusi II.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa an umarci ƴan Kwankwasiyya su runtuma fadar Sarkin domin dakile sake dawo da Aminu a ado Bayero kan sarautar jihar.

Umarnin Abba na cafke Aminu Ado Bayero

Wannan na zuwa ne yayin da Gwamna Abba Kabir ya umarci cafke tsohon sarkin bayan ya shigo garin Kano.

Gwamna Abba na zargin Aminu Ado da neman ta da hankulan jama'ar jihar bayan tube shi daga sarauta.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ɗauki zafi, ya ba da umarnin a kama tsohon Sarkin Kano

Aminu Ado Bayero ya shigo garin Kano ne da asubahin yau Asabar 25 ga watan Mayu inda ya yi salla a filin jirgin sama.

An karo sojoji domin kare Aminu Ado

A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojoji sun ba tsohon Sarki Aminu Ado Bayero kariya a Kano bayan tube shi a sarauta.

Daukar matakin ya biyo bayan umarnin Gwamna Abba Kabir na cafke tsohon sarkin da ya shigo garin Kano.

Wannan na zuwa ne bayan umarnin da Gwamna Abba Kabir ya bayar na cafke tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero a yau Asabar 25 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel