Gwamna Abba Ya Ɗauki Zafi, Ya Ba da Umarnin a Kama Tsohon Sarkin Kano
- Abba Kabir Yusuf ya bai wa kwamishinan ƴan sanda umarnin kama tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero cikin gaggawa
- Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bisa zargin tsohon sarkin da yunkurin tayar da tarzoma da ruguza zaman lafiya
- A jiya Alhamis da daddare ake tsammanin Aminu Ado Bayero ya dawo cikin Kano kwanaki biyu bayan Gwamna Abba ya tuɓe shi daga sarauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a kama tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero cikin gaggawa.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar da sanyin safiyar yau Asabar, 25 ga watan Mayu.
Gwamna Abba Kabir ya zargi tsohon sarkin da aka tsige da yunƙurin ta da zaune tsaye da haifar da tashin hankali a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aminu Bayero ya koma Kano
Sanarwar ta ce a daren jiya ne aka shigo da tsohon Sarkin cikin birnin Kano a yunkurin komawa fada da ƙarfi da yaji bayan kwana biyu da Gwamna ya sauke shi.
Dawakin Tofa ya bayyana cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya isa fadarsa da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar dare ranar Asabar, 25 ga watan Mayu, 2024.
Mai marataba sarkin ya shiga fada ne tare da rakiyar Mai Girma Gwamna Abba, mataimakin gwamna, kakakin majalisar dokokin jihar Kano da wasu manyan jami'an gwamnati.
Abba ya umarci a kama tsohon sarki
“A matsayinsa na babban kwamandan tsaro na jiha, mai girma gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umurci kwamishinan ‘yan sanda ya kama tsohon sarkin nan take.
"Gwamna ya umarci Kwamishinan ‘yan sanda ya kama tsigaggen Sarkin cikin gaggawa bisa zargin tada hankalin jama’a da yunkurin ruguza zaman lafiya da jihar ke ciki."
- Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan Gwamna Abba ya tsige Aminu Ado Bayero kana ya maye gurbinsa da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.
Sanusi II ya taɓo waɗanda suka tsige shi
A wani rahoton kuma Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ki yin magana kan masu hannu a tuɓe shi daga kan sarautar Kano a shekarar 2020.
Jim kaɗan bayan karɓar takardar aiki, Sanusi II ya bayyana cewa waɗanda suka yi masa hakan, ba su kai darajar da zai yi magana a kansu ba.
Asali: Legit.ng