'Yan Bindiga Sun Farmaki Ƴan Majalisa 5, Sun Buɗe Masu Wuta a Arewacin Najeriya

'Yan Bindiga Sun Farmaki Ƴan Majalisa 5, Sun Buɗe Masu Wuta a Arewacin Najeriya

  • Ƴan majalisa biyar sun tsallake rijiya da baya yayin da wasu ƴan bindiga suka buɗe masu wuta a hanyar komawa birnin Makurdi
  • Ganau sun bayyana cewa maharan sun fara shiga kauyen Tyomu kafin daga bisani su fara tare matafiya a titin Gboko zuwa Makurɗi a jihar Benuwai
  • Mai magana da yawun majalisar dokokin jihar Benuwai ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya nuna damuwa kan yawaitar hare-haren ƴan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Wasu miyagun ƴan bindiga sun farmaki tawagar mambobi biyar na majalisar dokokin jihar Benuwai a kan titin Makurɗi zuwa Gboko.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ƴan bindigar sun kai wa ƴan majalisar hari da misalin ƙarfe 10:00 a dare a daidai kauyen Tyomu mai nisan kilomita 16 zuwa Makurɗi.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye zauren majalisa yayin da rigama ta kaure

Gwamna Alia na jihar Benue.
Yan bindiga sun buɗe wa motocin ƴan majalisa 6 wuta a Benue Hoto: Fr. Hycinth Iormem Alia
Asali: Facebook

A cewar waɗanda suka shaida lamarin, maharan sun fara kai farmaki kan mazauna ƙauyen kafin daga bisani suka koma kan matafiyan da ke wucewa a titin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda harin ya rutsa da ƴan majalisa

Ɗaya daga cikin ƴan majalisar da harin da rutsa da su, Saater Tiseer, shugaban masu rinjaye a majalisar Benuwai ya tabbatar da lamarin ga wakilin Daily Trust.

Ya ce sun faɗa tarkon maharan ne yayin da suke kan hanyar dawowa daga wurin wani aiki a Gboko.

Honorabul Tiseer ya bayyana cewa bisa sa'a sun tsira daga mummunan harin ƴan bindigar lami lafiya, babu wanda ya samu ko kwarzane.

Majalisar Benue ta tabbatar da harin

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar Benuwai, Elias Audu, ya ce an kai wa ƴan majalisar hari da ƙarfe 10:00 na dare a hanyarsu ta dawowa daga ƙaramar hukumar Katsina-Ala.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya faɗi yadda suka shirya tsige sarakuna 5 da Ganduje ya naɗa a Kano

Ya ce sun je yankin ne domin jin ra'ayoyin jama'a game da kudirin kafa rundunar ƴan sa'kai ta jiha wanda za ta kare rayukan fararen hula, in ji rahoton Punch.

Audu ya bayyana cewa maharan da yawansu ya haura 40 a kan babura sun yi wa ‘yan majalisar kwanton bauna a Tyomu inda suka budewa motocin su wuta.

Ya jero ‘yan majalisar da abin ya shafa da su hada da, shugaban masu rinjaye, Saater Tiseer, mai tsawatarwa, Ipusu Bemdoo, mamba mai wakiltar Logo, Samuel Jiji, takwaransa na mazabar Mata, Simon Gabo da Cephas Dyaku.

Audu ya nuna damuwa kan yadda mazauna yankin Tyomu da Mbakera suka shafe kwanaki suna fama hare-hare, inda ya bukaci jami’an tsaro su cece su.

Ƴan bindiga sun kashe 11 a Benue

A wani rahoton kun ji cewa Akalla mutane 11 ne 'yan bindiga suka kashe a wani hari da suka kai kauyen Ole’Adag’aklo da ke gundumar Usha a jihar Benue.

Shugaban karamar hukumar Agatu, Yakubu Ochepo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce 'yan bindigar sun tafi da wasu da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262