Ministar Tinubu Ta Ji Wuta, Ta Ba da Tulin Kyaututtuka Ga Ƴan Mata 100 da Za a Aurar

Ministar Tinubu Ta Ji Wuta, Ta Ba da Tulin Kyaututtuka Ga Ƴan Mata 100 da Za a Aurar

  • Daga karshe, Ministar mata ta goyi bayan aurar da ƴan mata marayu 100 da aka shirya yi a jihar Niger da kakakin Majalisa ya dauki nauyi
  • Uju Kennedy-Ohanenye ta ba da tallafin kayan abinci da zannuwa da na karatu ga yan matan domin tallafa musu a rayuwarsu
  • Wannan na zuwa ne bayan kalubalantar auren da ta yi tun farko inda ta sha alwashin hana lamarin da ta kira take hakkin dan Adam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta ba da tallafin karatu ga yan mata marayu 100 a jihar Niger.

Uju ta kuma ba da kyaututtuka ga yan matan ana daf da aurensu bayan ta kalubalanci auren tun farko.

Kara karanta wannan

29 ga Mayu: Ministoci na cikin matsala, Tinubu ya basu umarni kan ayyukansu

Ministar Tinubu ya yi amai ta lashe kan auren mata marayu 100
Ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta tallafa da kaya a auren mata marayu 100 a Niger. Hoto: Uju Kennedy-Ohanenye.
Asali: Facebook

Ministar Tinubu ta bada tallafi a Niger

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminta na musamman, Adaji Usman ya fitar a yau Juma'a 24 ga watan Mayu, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adaji ya ce Ministar ta ba da tallafin kayayyaki na abinci da zannuwa da kuma na karatu ga ƴan matan idan suna sha'awar karin karatu har Jami'a.

Ministar ta mika kyaututtukan ne ta hannun hadiminta wanda aka gudanar a fadar Sarkin Kontagora, Mohammed Mu'azu.

Daga cikin kayan da ta bayar akwai zannuwa 100 da na'urar 'POS' guda 10 da buhunan shinkafa masu nauyin kilo 10 guda 350, cewar rahoton The Sun.

"Ba a fahimce ni ba ne" - Uju

Har ila yau, Ministar ta yi alkawarin ba da tallafin karatu har zuwa Jami'a ga dukkan ƴan matan idan suna bukata.

"Dukkan iyaye suna son aurar da yayansu idan har sun kai munzalin aure, ba a fahimci dalilin kalubalantar da na yi tun farko ba ne."

Kara karanta wannan

Yayin da ya ke jimamin mutuwar mahaifiyarsa, Kotu ta tausayawa Abba Kyari

"Kafofin sadarwa sun hada rigima tsakanina da kakakin Majalisa."

- Uju Kennedy-Ohanenye

Rijiyar Lemo ya gargadi Ministar Tinubu

Kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya gargadi Ministar mata kan shiga lamarin aure a jihar Niger.

Malamin ya ce bai kamata wacce ba ta san al'adu da addinin Hausawa ba ta tsoma baki a irin wannan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel