Tinubu Zai Kaddamar da Jirgin Kasan Abuja, Ya Yi Albishir 1 Ga Yan Najeriya

Tinubu Zai Kaddamar da Jirgin Kasan Abuja, Ya Yi Albishir 1 Ga Yan Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar da za ta kaddamar da sabon titin jirgin kasan Abuja domin fara jigilar fasinja
  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya sanar da haka a jiya Alhamis yayin taron bayyana nasarorin gwamnatin Bola Tinubu
  • Nyesom Wike ya yi albishir ga mazauna Abuja kan tanadin da gwamnatin ta yi musu domin amfani da jirgin kyauta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezonwo Wike ya ya sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta yafe kudin amfani da jirgin kasan Abuja da ake kokarin kaddamarwa.

Abuja
Tinubu zai kaddamar da sabon jirgin kasa a Abuja. Hoto: Aiwaju Bola Ahmed Tinubu|Railway Staff Forum
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ministan ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya ba da umurnin.

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

Mista Wike ya bayyana lamarin ne a ranar Alhamis a lokacin da ake taron bayyana irin kokarin da gwamnatin Bola Tinubu ta yi cikin shekara guda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za kaddamar da jirgin kasan?

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin ƙaddamar da jirgin a ranar 27 ga watan Mayu, 2024.

Daga nan ne kuma za cigaba da amfani da shi ba tare da biyan kudi ba har na tsawon wata biyu masu zuwa, rahoton the Cable.

Kaddamarwa sau biyu: Wike ya yi bayani

Kasancewar tsohuwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi bikin kaddamar da jirgin kasan, ministan ya yi karin haske.

Wike ya bayyana cewa duk da tsohuwar gwamnatin ta kaddamar da jirgin kasan, amma har ta wuce mutane ba su fara amfani da shi ba.

An yi gyare-gyare a titin jirgin

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi makudan kudin da za a kashe domin farfado da kamfanin Ajaokuta

Ministan ya kuma bayyana rashin samar da hanyoyin ababen hawa kan abin da ya hana jirgin kasan fara aiki tun da aka ƙaddamar da shi.

Amma a yanzu haka ya tabbatar da cewa an kammala samar da hanyoyi da za su saukaka zirga-zirgar ababen hawa a inda jirgin kasan yake.

Za a kaddamar da layin dogon Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa layin dogo da aka gina daga Legas zuwa Kano zai fara aikin jigilar kayayyaki a watan Yunin 2024.

Hakan ya fito fili ne a yayin wata ziyara da ministan sufuri, Saidu Alkali ya kai zuwa jihar Kano domin duba cigaban aikin layin dogon.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel