Wata Budurwa Ta Koka, Ta Wallafa Bidiyon Abin da Kwandasta Ya Mata a Cikin Mota

Wata Budurwa Ta Koka, Ta Wallafa Bidiyon Abin da Kwandasta Ya Mata a Cikin Mota

  • Wata budurwa ƴar Najeriya ta ja hankalin jama'a a soshiyal midiya bayan ta wallafa faifan bidiyon wani kwandastan motar bas
  • A faifan bidyon, an ga kwandastan yana ɗaure fuska da shiga yanayin ban dariya, lamarin da ya tsorata wasu fasinjojin da ke cikin motar
  • Mutane da dama da ke amfani da manhajar TikTok sun mayar da martani game da abubuwan da yaron motar ya yi a faifan bidiyon

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wata matashiyar budurwa ta bayyana abin da wani kwandasta ya masu yayin da ta shiga wata motar bas ta haya.

A faifan bidiyon da ta wallafa, an ga yaron motar ya canza fuska zuwa abu mai ban tsoro amma da nufin bada dariya a lokacin da motar ke tsaka da tafiya.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun yi magana kan sake maɗa Sanusi II a matsayin Sarkin Kano

Kwandastan mota.
Kwandasta ya tsorata fasinjoji ana tsaka da tafiya Hoto: @Foodietola
Asali: TikTok

Abin da yaron motar ya aikata

Budurwar wadda tana ɗaya daga cikin fasinjojin motar ta wallafa bidiyon abin da ya faru a shafinta na TikTok.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya nuna kwandastan motar ya ɗaure fuska kamar an masa wani abu da ya fusata shi ya hau sama.

Ya ci gaba da sauyawa zuwa fuskokin ban dariya da yin wasu abubuwa wanda ya sa mutanen cikin motar suka tsorata kuma suka nishadantu a lokaci guda.

Tola, wacce ta wallafa bidiyon a kan TikTok, ta ce ta tsorata sosai har ta kusa tsurewa a cikin motar saboda tsoro.

A cewarta, sun riga sun shiga motar an fara tafiya kuma sun biya kwandastan kuɗi lokacin da ya fara yin abubuwan da ba su taɓa tsammani ba.

Mutane sun yi martani kan bidiyon

@Daddyoo billion ya ce:

"Ba komai ake aminta da shi ba Najeriya, sai ya zare makami ya fara sararku sannan ido zai raina fata."

Kara karanta wannan

"An yaudare ni": An fasa daura aure bayan ango ya gano amarya ta yi ciko a mazaunai

@Bowtt ta ce:

"Lallai kun shiga motar Jakie Chan yau taɓ."

@FINE WINE ya ce:

"Lallai ne kuna da ƙarfin zuciya da har kuka iya zama kuna masa bidiyo, da nine tuni na kama kaina."

Matashi ya gano hanya a Tapswap

A wani labarin kun ji cewa wani dan Najeriya ya samar da mafita ga matsalar shiga Tapswap da yawancin 'yan Najeriya ke fuskanta a kwanan nan.

Ya fadi sunan manhajar sadarwar da 'yan Najeriya za su iya saukewa domin shiga Tapswap da kuma tara sulalla 1.5m a nan take.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel