Budurwa Ta Koka, Ta Ce Tana Son Ta Yi Aure Kafin Ta Mutu, Bidiyon Ya Bazu

Budurwa Ta Koka, Ta Ce Tana Son Ta Yi Aure Kafin Ta Mutu, Bidiyon Ya Bazu

  • Wata budurwa ta ce tana son ta yi aure kafin ta bar wannan duniyan duk da irin labarin da ta ke ji game da aure
  • Budurwar ta wallafa bidiyo a TikTok, tana mai cewa rashin aure abu ne mai damuwa da ban tsoro
  • Masoyanta a TikTok sun yi ta mata addu'a da bata shawarwari na karfafa gwiwa, suna fatan ta samu miji a 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Saboda halin rashin aure da ta tsinci kanta a ciki, wata budurwa yar Najeriya mai suna Chris Amrah a dandalin sada zumunta ta koka kan cewa za ta shiga 2023 ba tare da aure ba.

Amrah ta ce tana fatan ta samu mijin aure saboda ta ji abin da ake ji a rayuwar aure.

Chris Amrah
Budurwa Ta Koka, Ta Ce Tana Son Ta Yi Aure Kafin Ta Mutu, Bidiyon Ya Bazu. Hoto: Photo credit: TikTok/@baby..amrah.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Ajiye Girman Kai, Ta Isa Gaban Saurayinta Da Zobe Domin Neman Aurensa, Hotuna Sun Yadu

A cewar ta, tana son ta jin yadda yi wa miji biyayya ya ke a aure, ta yi kira ga mata su manta da batun gwagwarmayar 'neman kwato yancin mata wato feminism'.

Amma, ta yi godiya ga Allah bisa lafiya da rayuwa, amma ta koka da cewa rashin ganin kanta a gidan miji yana damunta a bidiyon da ta fitar.

Ta rubuta:

"Gaskiya bana son in mutu ba tare da dandana rayuwar aure ba... rashin aure, wannan wani abu ne da ke bani tsoro."

Ga dai bidiyon a kasa:

Kawo yanzu kimanin mutane 147k sun kalli bidiyon kuma wasu daga cikin masu amfani da soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakinsu.

Ga wasu daga cikin tsokacin da mutane suka yi:

Rashida Kamagate:

"Da izinin Allah za ka yi aure idan Allah ya so"

Khadijatgambo:

"Gaskiya mai daci. Allah ya bamu abokin zama na gari"

Salisu Usman:

Kara karanta wannan

"Ta Hanyar Kyakkyawar Niyya": Matashiyar Budurwa Ta Fice Daga Makaranta, Ta Samu N2.1bn a Cikin Wata Shida

"Allah ya baki mijin da za ku fahimci juna"

Dadie williams mike:

"Ki cigaba da kokari, za ki yi"

mustaphaaliyu203:

"Allah ya baki miji na gari"

abdulazizmusa639:

"Wanda Allah ya zaba miki na nan zuwa insha Allah"

ambernego:

"Shin akwai wani dalilin da yasa ba ki yi aure bane?"

Nasiha.yakub:

"Allah ya amsa addu'ar ki."

Open De man:

"Da fatan da gaske ki ke yi. Allah ya baki miji wanda zai so ki a kowanne lokaci kuma ku fahimci juna cikin soyayya da imani."

aishasuleimann3:

"kada ki damu sosai yar uwa. gara ba ki da aure da yin aure mara kyau. bai dace a yi gareje kan lamarin aure ba. ki yi addu'a, wanda ya dace da ke zai taho."

Asali: Legit.ng

Online view pixel