Bidiyon Lokacin da Ganguje Yake Shaguɓe ga Muhammadu Sanusi II Bayan Tube Shi
- Yayin da aka rushe masarautun Kano, an gano wani tsohon bidiyo da ake shagube ga Khalifa Muhammadu Sanusi II
- Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje shi ne ke yin dariya a cikin faifan bidiyon bayan tube Sanusi a 2020
- Wannan na zuwa ne bayan sake mayar da Muhammad Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano da Abba Yusuf ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - An bankado wani tsohon bidiyo da tsohon gwamnan Kano ya ke shagube ga Muhammad Sanusi II.
Hakan ya biyo bayan rushe masarautun Kano guda biyar a yau Alhamis 23 ga watan Mayu 2023.
Ganduje ya yi amfani da dabarar Jonathan
A cikin faifan bidiyon, Ganduje ya bayyana yadda ya tube Sanusi daga kujerar sarauta ta hanyar amfani da dabarar Jonathan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban na jam'iyyar APC ya ce ya yi amfani da maganin Jonathan kan Sanusi domin kawo gyara a masarautar Kano.
Wani mai amfani da kafar sadarwa ta X, @emmaikumeh shi ya yada faifan bidiyon da Ganduje ke cin mutunci ga Sanusi.
Abin da Ganduje ke cewa a bidiyo
"Lokacin da na zama gwamna, a nan ne za ku yi dariya, na ce eh maganin Jonathan."
"Magani ne mai kyau, duk da ni ba likita ba ne, amma zai yi amfani a kan cutar da kuma shi marar lafiyan."
"Na yi amfani da dabarar maganin Jonathan na yi amfani da shi domin kare masarautu kuma na yi amfani da shi yadda ya dace."
- Abdullahi Ganduje
Har ila yau, Gwamna Abba Kabir ya dawo da Muhammadu Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano bayan rusa masarautun jihar guda biyar da Majalisar dokoki ta yi a yau Alhamis 23 ga watan Mayu.
Majalisar Kano ta rushe masarautun jihar 5
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Kano, ta rusa masarautun jihar guda biyar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.
Majalisar ta dauki matakin ne a yau Alhamis 23 ga watan Mayu inda ta bukaci Gwamna Abba Kabir ya sanya hannu.
Daga bisani Abba ya sanya hannu a dokar da ta tabbatar da korar Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna daga sarautar jihar Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng