“An Gyara Zalunci”: 'Dan Sanusi II Ya Magantu da Majalisa Ta Rusa Masarautun Kano

“An Gyara Zalunci”: 'Dan Sanusi II Ya Magantu da Majalisa Ta Rusa Masarautun Kano

  • Ashraf Sanusi, dan tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan rusa masarautu biyar tare da tsige sarakuna
  • Ya ce matakin da majalisar dokokin jihar Kano ta dauka, gyara ne ga zaluncin da aka yi wa mahaifinsa shekaru biyar da suka wuce
  • Ashraf ya yi wa mahaifinsa, Sanusi II addu’a, yana mai cewa Allah ya kara masa tausayi, ya kuma kara masa tsoron Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano Ashraf Sanusi, dan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce majalisar dokokin jihar Kano ta gyara rashin adalci da aka yi ta hanyar soke masarautu biyar na jihar.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani ga sanarwar da ‘yan majalisar dokokin jihar suka yi na tsige sarakunan sababbin masarautun guda biyar.

Kara karanta wannan

"Wannan ba cigaba ba ne': Hadimin Buhari ya caccaki Majalisa kan rusa masarautun Kano

Dan Sanusi ya yi magana bayan majalisa ta rusa masarautun Kano
Dan Sanusi ya ce rusa masarautun Kano gyara ne na rashin adalcin da aka yi wa mahaifinsa. Hoto: Ashraf Sanusi
Asali: Instagram

Maganar Ashraf Sanusi II a Instagram

'Dan sarkin ya bayyana haka ne ta shafin sa na Instagram @AsrafSanusi a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ashraf ya yi addu'ar Allah ya kubutar da mahaifinsa daga makircin mayaudara, ya kuma ba shi damar yin nasara ba tare da sun iya tabuka komai ba.

Ya rubuta cewa:

“Ya Allah, kai ne ke ba da mulki ga wanda ka so, kuma ka karbe mulki daga hannun wanda ka so, kuma kai ke shiryar da wanda ka so, kuma ka tabar da wanda ka so.
Duk abin da ka yi dai dai ne Ya Allah. Yau ga shi cikin buwayarka ka sa an gyara zaluncin da aka yi a baya.
Ya Allah ka kare Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga sharrin masu sharri."

Sanusi II zai koma sarautar Kano?

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnan PDP ya taya Muhammadu Sanusi II murna game da dawowa karaga

Tun da fari, mun ruwaito cewa mai martaba Sarkin Kano na 14, Alhaji Muhammadu Sanusi II na kan hanyarsa ta komawa kan karagar mulki.

An tsige Sanusi II ne a shekarar 2020 bayan ya yi takun saka da tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa ana jira ne kawai gwamnan Kano, Abba Yusuf ya sa hannu kan dokar rusa masarautun jihar domin dawo da Sanusi II kan kujerarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel