Majalisar Kano Ta Rusa Duka Sarakunan da Gwamnatin Ganduje Ta Kirkiro a 2019
- A karshe, Majalisar jihar Kano ta rushe masarautun da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkira a lokacin mulkinsa
- Majalisar jihar ta dauki wanann matakin ne a yau Alhamis 23 ga watan Mayu bayan dokar ta tsallake karatu na uku
- Legit Hausa ta tattauna da jigon PDP kuma tsohon dan takarar majalisar dokokin Kano kan wannan lamari
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da rushe masarautun da tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.
Majalisar ta dauki wannan matakin ne a yau Alhamis 23 ga watan Mayu yayin zaman majalisar a Kano.
An rushe masarautun Ganduje a Kano
Sarakunan da abin ya shafa su ne wadanda Ganduje ya kirkira lokacin da yake kan madafun iko a jihar, cewar Freedom Radio.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun farko an sanya yau Alhamis 23 ga watan Mayu cewa majalisar dokokin Kano za ta yi duba tare da yanke hukunci kan kudirin gyaran dokar masarautun jihar.
Dukkan wadanda aka nada ko karawa girma a tsohuwar dokar za su koma matakin da suke tun farko, cewar Daily Trust.
Kano: 'Dan majalisa ya gabatar da kudiri
Shugaban masu rinjaye a majalisar, Hussaini Lawal Chediyar Yan Gurasa ya gabatar da kudirin a gabanta.
Lawal da ke wakiltar mazabar Dala ya bukaci rushe masarautun guda biyar da Ganduje ya kirkiro a ranar 5 ga watan Disambar 2019.
Masarautun sun hada da Kano da Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye inda wani ɗan Majalisar da ya boye sunansa ya ce babu wanda ya isa ya hana aiwatar da dokar.
Legit Hausa ta tattauna da jigon PDP
Legit Hausa ta tattauna da jigon PDP kuma tsohon dan takarar majalisar dokokin Kano.
Hon. Adnan Mukhtar Tudun Wada ya yi Allah wadai da mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarauta.
Ya ce ba a gyara barna da barna inda ya ce an mayar da sarauta da dawo siyasa ganin cewa Abba Kabir ya yi abin da mai gidansa Rabiu Kwankwaso ke so.
"Wannan lamari ya dawo siyasa kuma shi Sarki bai kamata da girmansa ya zama ɗan siyasa ba, muna Allah wadai da hakan ganin an siyasantar da masarauta."
"Masarautun da aka kirkira a Rano da Gaya da Karaye da kuma Bichi ci gaba ne ga al'ummarsu, ya kamata a bar wa mutanen ƙauyukan nan sarakunansu."
"Mu yan siyasa muna ganin harkar ta koma wa'adi wanda ba ma fatan a lalata harkar saboda a gaba za a iya sauya Sanusi II saboda siyasa."
- Adnan Mukhtar
Adnan ya bukaci jama'a da su fita su karbo katin jam'iyya saboda jam'iyyun APC da NNPP sun gaza, al'umma suna cikin yunwa da rashin ruwa amma gwamnati ta kau da hankalin mutane da maganar sarauta.
Ƴan majalisar APC sun fusata a Kano
A wani labarin, kun ji cewa 'yan jam'iyyar APC a majalisar dokokin jihar Kano sun ɗauki matakin ficewa daga zauren majalisar a yau Alhamis 23 ga watan Mayun 2024.
Ƴan majalisar na jam'iyyar adawar a jihar Kano sun fice daga majalisar ne yayin zaman majalisar take gudanarwa na ranar Alhamis.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng