Jerin Ƴan Arewacin Najeriya 8 da Suka Fi Kowa Arziki a Yankin
A Najeriya, akwai hamshakan masu arziki wadanda suka hada da ƴan Arewacin kasar da ke da tulin dukiya na gani a fada.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Daga cikin hamshakan attajirin da ke Arewacin Najeriya har da Aliko Dangote wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka.
Legit Hausa ta binciko muku ƴan kasuwa da ƴan siyasa a Arewacin Najeriya da suka fi kowa kudi.
1. Aliko Dangote
Attajiri Aliko Dangote wanda ɗan asalin jihar Kano ne, shi ne wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka da kudi $13.9bn, cewar BusinessDay
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote mai shekaru 66 yana da kamfanin siminti da ya ke jagoranta da na sukari da matatar mai da sauran kayan masarufi.
Attajirin ya dauki ma'aikata a kamfanoninsa fiye da 11,000 a yanzu yayin yake hasashen daukar ma'aikata fiye da 30,000 a matatar mansa da ke Lagos.
2. Abdussamad Rabiu
Alhaji Abdussamad Rabiu wanda ya mallaki $5.9bn shi ma ya fito daga jihar Kano wanda ke jagorantar kamfanin BUA.
Attajirin mai shekaru 63 yana da kamfanin siminti da sukari da samar sauran kayan abinci yayin da yake taimakawa marasa karfi ta hanyar gidauniyarsa.
3. Ibrahim Badamasi Babangida
An haifi Janar Ibrahim Badamasi Babangida a ranar 17 ga watan Agustan 1941 a jihar Niger.
Babangida ya mulki Najeriya daga shekarar 1985 zuwa shekarar 1993 bayan kifar da gwamnatin Muhammadu Buhari.
Ana jita-jitar Babangida yana da $5bn inda aka tabbatar yana da wasu kadarori na biliyoyin daloli.
4. Alhaji Dahiru Mangal
Dahiru Mangal yana daga cikin attajirai a Arewacin Najeriya wanda ya fito daga jihar Katsina.
Fitaccen dan kasuwar yana da kudi $2.2bn inda yafi ba da karfi wajen harkokin jiragen sama da sauran lamura na kasuwanci a Arewacin Najeriya.
5. Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fara kasuwanci tun yana aiki da hukumar Kwastam a Najeriya, yana kudi ya kai $1.6bn.
Atiku ya tsunduma harkar kasuwanci daban-daban daga cikin abin da ya mallaka har Jami'ar AUN da ke Yola a jihar Adamawa.
6. Danjuma Theophilus
An haifi Theophilus Yakubu Danjuma a ranar 9 ga watan Disambar 1938 a jihar Taraba wanda shi ne shugaban kamfanin South Atlantic Petroleum (SAPETRO), an ƙiyasta kudinsa ya kai $1.2bn, cewar Punch.
Danjuma ya kasance tsohon soja kuma ɗan siyasa wanda ya rike mukamin hafsan sojoji daga 1975 zuwa 1978 kafin rike mukamin Minista a mulkin Cif Olusegun Obasanjo.
7. Mohammed Indimi
An haifi Mohammed Indimi a ranar 12 ga watan Agustan 1947 a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Ndimi wanda bai samu halartar makarantar boko ba amma ya fantsama cikin harkokin kasuwancin man fetur, yana da akalla kuɗi kusan $1bn.
8. Aminu Dantata
Attajirin Aminu Dantata ya fito ne daga jihar Kano wanda ya ke jagorantar kamfanoni da dama wanda kudinsa ya kai $1bn.
An haifi attajirin a ranar 19 ga watan Mayun 1931 wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin inganta ilimin marasa karfi da taimakawa masu kananan karfi
Kasashen da ke amfani da harshen Hausa
Kun ji cewa akwai wasu ƙasashe a Nahiyar Afirka da dama da ke amfani da yaren Hausa bayan Najeriya da ke Yammacin Nahiyar.
Mafi yawan wadannan Hausawa sun je kasashen ne domin neman kudi sanadin kasuwanci da sauran dalilai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng