Gwamnan Kano ya Kafa Kwamitin Bincike Saboda Yawan Faduwa Jarrabawar 'Qualifying'

Gwamnan Kano ya Kafa Kwamitin Bincike Saboda Yawan Faduwa Jarrabawar 'Qualifying'

  • Gwamnatin Kano ta kafa wani kwamitin da zai bincike mummunar faduwa da daliban jihar kimanin 103,777 suka yi a jarrabawar 'qualifying' da ya kammala a baya-bayan nan
  • Daliban aji biyar, wato SS2 a makarantun gwamnati na rubuta jarrabawar domin neman hukuma ta dauki nauyin su rubuta jarrabawar WAEC ko NECO idan sun yi nasara
  • Ana bukatar akalla dalibi ya yi nasara a darussa biyar ciki har da lissafi da turanci, sai dai a wannan karon an samu bullar labarin mummunar faduwa domin dalibai 28, 333 ne kawai su ka yi nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano-Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin da zai binciki dalilin da ya janyo daliban makarantun sakandiren jihar nan suka yi mummunar faduwa a jarrabawar 'qualifying'.

Kara karanta wannan

Saura kwanaki 2: Abubuwan da dalibai za su tanada kafin samun lamunin karatu

Daliban makarantun gwamnati da ke ajin SS2 ne ke rubuta jarrabawar, wanda idan sun yi nasarar a darussa biyar ciki har da lissafi da turanci, gwamnati na daukar nauyin su rubuta jarrabawar WAEC da NECO.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa wannan na kunshe cikin sanarwa da darakatan yada labaran ma’aikatar ilimi a jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar.

Aikin da kwamitin binciken zai yi

Daga ayyukan da aka dorawa kwamitin akwai kokarin gano yawan munin faduwar da daliban suka yi, da gano musabbabin faduwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zantawarsa da Legit Hausa ta wayar hannu, Balarabe Abdullahi ya bayyana za a samar da alkaluman wadanda su ka fadi jarrabawar.

The Nation ta ruwaito cewa kwamitin zai yi bincike kan ko ana bin ka’idojin da gwamnati ta sanya na fitar da sakamakon kowace jarrabawa a jihar.

Kara karanta wannan

Shugaban makaranta ya tsere da kudin jarrabawar WAEC da NECO, ya lula kasar waje

Balarabe Kiru ya ce, kwamitin zai kuma binciki yadda aka yi daliban da ba na makarantun gwamnati ba suka rubuta jarrabawar.

A cewar sanarwar kwamitin zai samu jagorancin Alhaji Tajuddeen Gambo, wanda shi ne mataimaki na musamman ga gwamnan Kano a kan harkar ilimi kuma tsohon kwamishinan ilimin jihar nan, tare da ba kwamitin kwanaki bakwai ya mika rahotonsa.

Gwamnati ta bude kafar neman rancen karatu

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin tarayya na daf da bude shafin intanet domin bawa dalibai daman fara neman rancen karatu.

Shugaban asusun NELFUND da ke da alhakin kula da raba lamunin ya lissafa ka'idojin da za a bi wajen neman rancen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel