Yayin da Ya Ke Jimamin Mutuwar Mahaifiyarsa, Kotu Ta Tausayawa Abba Kyari

Yayin da Ya Ke Jimamin Mutuwar Mahaifiyarsa, Kotu Ta Tausayawa Abba Kyari

  • Yayin da ya ke jimamin mutuwar mahaifiyarsa, Abba Kyari ya samu belin makwanni biyu daga babbar kotun tarayya
  • Kotun da ke zamanta a Abuja ta ba da belin Kyari ne a yau Laraba 22 ga watan Mayu kan zargin safarar kwayoyi
  • Wannan na zuwa ne bayan hukumar NDLEA ta gurfanar da shi a gaban kotun tun a watan Faburairun 2022

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba tsohon dan sanda, DCP Abba Kyari belin makwanni biyu.

An ba Abba Kyari belin ne yayin da ya ke cikin jimamin mutuwar mahaifiyarsa da ta rasu a farkon watan Mayu da muke ciki.

Kara karanta wannan

Rikici ya kaure da aka bindige ɗan sanda a tsakiyar kasuwar Jos

Kotu ta bada belin Abba Kyari a Abuja
Kotun Tarayya ta ba da belin Abba Kyari na tsawon makwanni 2. Hoto: Hon. Usman Aminu.
Asali: Facebook

Belin kwanaki nawa Kyari ya samu?

Wannan mataki na kotun na zuwa ne bayan Kyari ya shafe watanni 27 a kulle kan zargin ta'ammali da safarar miyagun kwayoyi a cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun har ila yau, ta sanya ranar Juma'a 31 ga watan Mayu domin duba yiwuwar belinsa kan zargin wanda hukumar NDLEA ta gurfanar da shi, Leadership ta tattaro.

Hukumar ta na zargin Kyari da wasu jami'an ƴan sanda da karbar hodar iblis bayan sun cafke wasu da ake zargi da safarar kwayoyi.

An dakatar da Kyari a matsayin dan sanda

A shekarar 2022 ne dai hukumar yan sanda ta PSC ta dakatar da Abba Kyari da wasu jami'an ƴan sanda guda biyu.

Wadanda aka dakatar tare da Kyari sun hada da James Bawa da Sunday Ubua kan zargin safarar miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Lauyoyin Murja sun yi fatali da ita, sun fadi nadamar da suka yi a shari'arta

Daga bisani sai hukumar NDLEA ta ayyana neman Kyari ruwa a jallo kan alaka da masu safarar kwayoyi na kasa da kasa.

Mahaifiyar Abba Kyari ya rasu a Borno

Kun ji cewa, mahaifiyar DCP Abba Kyari, Mama Yachilla Kyari ta riga mu gidan gaskiya bayan shan fama da jinya a jihar Borno.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mahaifiyar jajirtaccen jarumin dan sandan da aka dakatar ta rasu a ranar Lahadi 5 ga watan Mayu.

Sai dai Kyari ba zai samu damar halartar jana'izar mahaifiyar tasa ba saboda yana kulle kan Qaisu zarge-zarge daga hukumar NDLEA.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel