An Tsure Bayan Dattijo Mai Shekaru 70 Ya Mutu a Cikin Kotu Yayin Ba da Shaida
- Wani dattijo mai shekaru 70 ya rasa ransa a cikin kotu yayin da ya je shi domin ba da shaida a jihar Ondo
- Lamarin ya faru ne a yau Laraba 22 ga watan Mayu a babbar kotun jihar da ke Oka yayin shari'a a kotun
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar haka a yau Laraba 22 ga watan Mayu inda ta ce sun dauki gawar dattijon
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - An shiga fargaba bayan wani dattijo ya fadi ya mutu a cikin kotu ana daf da fara gudanar da shari'a.
An kira dattijon mai shekaru 70 kotun da ke jihar Ondo ne domin ya ba da shaida kan wata rigima.
Yaushe dattijon ya mutu a kotu?
Lamarin ya faru ne a yau Laraba 22 ga watan Mayu a babbar kotun jihar da ke Oka kafin fara shari'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Nation ta tabbatar da cewa dattijon ya zo kotun ne domin ba da shaida kan wata shari'a da ake yi da abokinsa.
Wani ma'aikacin kotun ya ce dattijon da ba a bayyana sunansa ba ya fadi ne ba tare da wani abu ya faru tsakaninsa da wani ba, cewar Tribune.
"Dattijon yana kotu inda ya je ba da shaida da abokinsa, kawai ya fadi kasa inda ya buga kansa da siminti nan take ya mutu."
"Bai yi kama da wanda za a ce ba shi da lafiya ba, kuma bai yi wata rigima da wani ba da za a ce shi ne dalilin mutuwarsa."
- Ma'aikacin kotun
Ƴan sanda sun dauki gawar dattijon
Wani shaidan gani da ido, Tunde Ariyon ya ce dakarun 'yan sanda Enu-Owa sun karaso kotun domin daukar gasar marigayin.
Rundunar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce za a gudanar da bincike a hedkwatar hukumar da ke Akure.
Kotu ta tube sarki a Ondo
Kun ji cewa babbar kotu ta tube rawanin basaraken Owo, Oba Michael Adetunji, daga mukamin Sarkin Ute a karamar hukumar Ose ta jihar Ondo.
Oba Michael Adetunji Oluwole ya shiga takaddamar shari'a game da zamansa sarki tun a shekarar 1995.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng