EFCC Ta Bankado Badakalar N2.17bn a Lokacin Gwamnatin Goodluck Jonathan

EFCC Ta Bankado Badakalar N2.17bn a Lokacin Gwamnatin Goodluck Jonathan

  • Hukuma mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bankado badakalar da aka yi a lokacin shugaba Goodluck Jonathan
  • Ana zargin badakalar ta faru ne karkashin ofishin mai ba shugaba Jonathan shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki (Mai ritaya)
  • Dan kwangilar da ya karbi kudin ya bayyana yadda lamarin ya faru a zaman kotun da ya gudana ranar Litinin a birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Hukuma mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bankado badakalar kudi da ya faru lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.

Sambo
Dan kwangila ya amsa laifin karbar kudi wajen Sambo Dasuki. Hoto: Economic and Financial Crime Commission.
Asali: Facebook

EFCC ta tono 'badakala' a ofishin Dasuki

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Bola Tinubu ta jefa Najeriya cikin tsaka mai wuya," Dattijon Arewa

Hukumar EFFC ta bayyana a shafin ta na Facebook cewa badakalar ta faru ne karkashin ofishin mai ba shugaba Jonathan shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a shekarun baya dai hukumar EFCC ta gurfanar da Sambo Dasuki bisa karkatar da kudin makamai wanda har hakan ya kai shi ga zaman gidan yari.

N2.17b: EFCC ta kama dan kwangila

EFCC ta gurfanar dan kwangilar da ta kama mai suna Olugbbenga Obadina a ranar Litinin 20 watan Mayu.

Dan kwangilar ya tabbatar wa kotu cewa ya karbi zunzurutun kudi N2.17b daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a shekarar 2015.

An karbi N2.17bn babu dalili

Har ila yau a zaman kotun, dan kwangilar ya bayyana cewa ya karbi kudin ne ba tare da manufar gudanar da wani aiki ga gwamnatin tarayya ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake ba babban mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale sabon mukami

Ya kuma ƙaryata rade-radin da ke cewa an ba shi kudin ne domin ayyukan samar da wuta ta hanyar amfani da hasken rana a jihar Yobe.

Bayan sauraron karar da yin tambayoyi da wanda ake zargi, alkalin kotun mai Shari'a Nnamdi Dimgba ya daga shari'ar.

A ranar 30 ga watan Mayu kotun za ta zauna domin cigaba da sauraron karar da EFCC ta shigar kan zargin dan kwangilar da aikata laifuffuka takwas.

EFCC ta magantu kan Yahaya Bello

A wani rahoton, kun ji cewa Ola Olukoyede ya sha alwashin cewa zai yi murabus daga kujerar shugaban EFCC idan aka gaza gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu.

Shugaban EFCC ya kuma rantse da cewa zai bi diddigin shari'ar tsohon gwamnan jihar Kogi har zuwa lokacin da za a ƙarkare ta domin tabbatar da gaskiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel