Ba a Manta da Kisan Ummita a Kano Ba, Wani Ɗan China Ya Sake Kashe ’Yar Najeriya

Ba a Manta da Kisan Ummita a Kano Ba, Wani Ɗan China Ya Sake Kashe ’Yar Najeriya

  • Wata matashiya 'yar jihar Abia ta mutu bayan da wani dan kasar China da ake zargi ya tunkudo ta kasa daga saman babbar mota
  • Ana zargin cewa dan China, wanda ke aiki a kamfanin Inner Galaxy ya kashe Ocheze Ogbonna ne saboda kin amincewa da soyayyarsa
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da jimami a Arewa, bayan wani 'dan China ya kashe wata matashiya Ummita saboda soyayya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Abia - Ana zargin cewa wani dan kasar China ya kashe wata ma’aikaciyar kamfanin karafa na Inner Galaxy da ke jihar Abia.

Ana zargin dan China ya kashe 'yar Najeriya
Ana zargin wani dan China ya kashe wata matashiyar 'yar Abia saboda soyayya. Hoto: Desmond Nmeka Ifeanyi
Asali: Facebook

Ana zargin mutumin China da kisa

Miss Ocheze Ogbonna ta rasu ne bayan wani dan kasar Sin din ya tunkudo ta kasa daga saman wata babbar mota saboda kin amincewa da soyayyarsa.

Kara karanta wannan

'Banex Plaza': Soja ya shararawa wata mata mari har ta fada doguwar suma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar 'dan majalisar wakilai na mazabar Ukwa ta Gabas/Ukwa ta Yamma a jihar Abia ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

An nemi a bi kadin wadda aka kashe

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Nkwonta ya bayyana matukar bakin cikinsa game da kisan 'yar mazabarsa.

Ya kuma bayyana wannan aika-aika da ake zargin dan China ya yi na kashe matashiyar a matsayin mugun abin da ke daga hankali.

A yayin da yake tabbatar da cewa an san mazabarsa da zaman lafiya, dan majalisar tarayyar ya bukaci a yi adalci ga wadda aka kashe.

Matasa sun gudanar da zanga-zanga

Wani ma'abocin Facebook, Desmond Nmeka Ifeanyi ya ce matasan garin Umuahala Asa, inda aka haifi Miss Ocheze, sun mamaye kamfanin bayan mutuwar matashiyar.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan wasan Real Madrid, Toni Kroos, zai yi ritaya daga buga kwallon kafa

"Matasan garin da suka ji wannan mummunan al’amari sun mamaye kamfanin domin nuna rashin amincewarsu da mutuwarta, amma sojoji da ke tsaron kamfanin suka tarwatsa su."

'Dan China ya kashe Ummita a Kano

Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa wani dan kasar China mai suna Frank Geng Quarong ya kashe masoyiyarsa 'yar Najeriya, Ummukulsum Sani Buhari saboda sun daina soyayya.

Quarong ya yi ikirarin cewa Umiita tayi watsi da soyayyar shi bayan kashe mata makudan kudi a cikin shekaru biyun da suka yi tare da kuma yi masa alkawarin aure.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.